Kin jinin Musulmai: An bayyana kasar India a matsayin kasar da tafi kowacce kasa hatsari ga al’ummar Musulmai a duniya

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Kin jinin Musulmai: An bayyana kasar India a matsayin kasar da tafi kowacce kasa hatsari ga al’ummar Musulmai a duniya

An sanya kasar India a jerin kasashen da suka fi hadari ga musulmai, a fadin duniya

India din ta zama mai hadarin ne a karkashin mulkin kama karya na babban minista Narendra Modi.

Kafar yada labarai ta Kashmir Media, ta buga rahoto da yake nuna yadda India a karkashin mulkin Modi, ta zama wani wuri na barazanar kisan kare dangi ga musulmai, wanda tun bayan hawansa mulki ake samun karuwar tarzomar kin jinin musulmai. 

Rahoton ya wallafa cewa, shuwagabannin Hindutva ne suke iza wutar, Inda suke kira da a afkawa musulmai, a kashe su, a kasar ta India. 

Haka kuma rahoton ya kara da cewa, kiyayyar Modi din ga musulmai ta kara fitowa fili yayin da aka ayyana soke sanya hijabi. Wannan soke sanya hijabin alamace ta kiyayyar sa ga musulmai. 

Rahoton yace, a sakamakon boren da akayi na Gujarat a shekarar 2002, sakamakon kin jinin musulmai, kadai ya isa a ayyana Modi a cikin jerin azzaluman shugabanni a duniya. Saboda laifin da ya aikatawa musulmai. 

An soki babban minista Modi ne, domin  bada umarnin gididdiba musulmai a zanga-zangar Gujarat, da kuma mamaye Jammu da Kashmir ba bisa ka’ida ba. Kamar yadda rahoton ya bayyana.

Yadda wani bidiyo ya nuna ‘yan sanda a Indiya na dukan mata Musulmai da suka fito yin zanga-zangar hana su sanya Hijabi

Yayin wata zanga-zangar adawa ta dokar hana sa hijabi a Uttar Pradesh ta Ghaziabad da ke kasar Indiya an ga ‘yan sandan jihar sun farwa mata Musulmai da ke sanye da hijab da duka.

Yayin da zanga-zangar ke cigaba da gudana a wasu da ga cikin jihohin kasar a bisa kan dokar hana sa hijabi a kwalejoji, hatsaniyar ta fara ne a Karnataka wanda har ta kai ga an shiga kotu.

Rundunar ‘yan sandan ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan faifan bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta inda wasu suke suka tare da caccakan ‘yan sandan.

Yan sanda sun gabatar da rahoto ga me da lamarin

Dangane da lamarin da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata, ‘yan sanda sun gabatar da rahoton farko game da bayanan abun da ya faru.

A rahoton da ‘yan sandan suka fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu labarin cewa wasu matan Musulmi kimanin su 15 dauke da takardu na nuna adawa da gwamnati sun taru a hanyar Sani Bazaar a Ghaziabad ba tare da an basu izini ba. FIR ta ruwaito cewa matan sun fara rera waka ne a lokacin da tawagar ‘yan sanda ta iso wurin.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun farma ‘yan sanda

Wasu maza da suka fito daga cikin tawagar masu zanga-zangar sun fito inda suka fara cin zarafi suna zagin jami’an ‘yan sandan da ke kokarin kora masu zanga-zangar su koma gida, a cewar FIR. A cewar korafin da ‘yan sandan su ka fitar an bayyana wani mai suna Raees a matsayin daya daga cikin wadanda ake tuhuma , kuma masu zanga-zangar sun yi barazana ga ‘yan sandan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi