Bayan shekaru 42 da tafiya neman arziki, tsoho mai shekaru 94 ya dawo gida wayam

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Bayan shekaru 42 da tafiya neman arziki, tsoho mai shekaru 94 ya dawo gida wayam
Bayan shekaru 42 da tafiya neman arziki, tsoho mai shekaru 94 ya dawo gida wayam

Wani tsoho ya dawo hannu Rabbana, bayan kwashe shekaru 42 yana neman arziki inda ya bar gidan sa da iyalan sa, LIB taruwaito.

Wani dan kasar Kenya mai shekaru 94, ya dawo ga iyalin sa da ke kauyen Majengo, a garin Mwatate da ke yankinTaita-Taveta bayan kwashe shekaru 42 yana neman arziki bayan ya bar gida.

hustler
Bayan shekaru 42 da tafiya neman arziki, tsoho mai shekaru 94 ya dawo gida wayam

Hiltan Kalugho ya bayar da labarin yadda ya tafi ya bar matarsa da yaransa guda bakwai a gida ya garzaya kasar Tanzania, kasar da ke makwabtaka da su a shekarar 1980 don neman arziki.

A cewarsa:

“Na bar gida na don neman kudin da zan rufa wa kai na asiri don in inganta wa yara na rayuwa . Sai dai, na kasa komawa gida saboda ban samu kudin da nake nema ba.”

Kamar yadda dattijon ya bayyana, ya yi rayuwar a iyakar birnin Mororoni, inda da farko ya fara aiki a matsayin mai hakar ma’adanai, bayan yaga babu wani samu sai ya koma kiwon dabbobi.

“Bayan na ga babu wata riba, kullum cikin kashe ‘yan kudaden nake sai na hakura,” a cewar Kalugho.

Kalugho ya ce, bai sake wani auren ba har ya yanke shawarar komawa gida.

Wani fasto dan kasar Kenya ya ziyarci yankin, bayan haduwa da Kalugho ya yada labarinsa a kafafan sada zumuntar zamani yana bukatar a taimaka mishi don sada shi da iyalinshi.

Dan Kalugho, Mnjala Mwaluma, ya ce bayan kwashe shekaru suna neman mahaifin su, wani fasto ya kira shi, inda ya sanar da shi cewa sun hadu a kasar Tanzania.

“Ban dade da samun kira daga fasto ba, na yi mamaki a lokacin da ya sanar da ni cewa ya ga mahaifi na a Tanzania. Ya wuce da ni Mombasa, daga nan muka hadu,” a cewar Mwaluma.

Kalugho ya dawo gida gida a makon da ya gabata, inda ya tarar matar sa da yaransa maza guda biyu duk sun rasu a shekarar 2007.

“Rai na ya sosu kwarai. Na cii burin ganin mata ta da duk yara na,” a cewarsa.

An kama tsohon Sanata da hannu a kisan shugaban kasa

An kama Jean Joel Joseph, tsohon dan majalisar dattawa na kasar Haiti wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin kisan shugaban kasar Jovenel Moïse a Jamaica. BBC ta ruwaito cewa hukumomin Jamaica a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, sun tabbatar da cewa sun kama Joseph ne a yammacin Juma’a, 14 ga watan Janairu.

Jami’in Constabulary Force dake Jamaica (JCF) a wata sanarwa sun bayyana cewa an kama Joseph ne tare da wasu mutane uku da ake zargin ‘yan uwansa ne kan laifin shige da fice. An bayyana cewa an kama joseph ne a wani gida a St. Elizabeth, wanda ke cikin wani karamin coci da ke kudu maso yammacin tsibirin.

A cewar majiyar ‘yan sandan Jamaica, Joseph yana tsare. ABC News ta ruwaito cewa kakakin ‘yan sanda Gary Desrosiers ya ki bayar cikake karin bayani game da kama shi da akayi.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi