An kama dan Najeriyan da ke tatsar kudin matan Indiya da sunan zai aure su

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing An kama dan Najeriyan da ke tatsar kudin matan Indiya da sunan zai aure su
An kama dan Najeriyan da ke tatsar kudin matan Indiya da sunan zai aure su

‘Yan sanda sun yi ram da wani dan Najeriya, tare da abokan sa biyu a kasar Indiya, bisa zargin su da damfarar mata inda suke musu alkawarin aure, LIB ta ruwaito.
An kamo mazan guda uku, tare da wani dan Najeriyaa garin Ghaziabad da ke Uttar Pradesh bisa zargin su da yaudarar mata ta hanyar kulla soyayya da su a kafafan sada zumuntan zamani.

mutan indiya
An kama dan Najeriyan da ke tatsar kudin matan Indiya da sunan zai aure su

Ana zargin Arvind Verma, Prince Pandey da hada kai dadan Najeriyan mai suna Didier.

Takardar da rundunar ‘yan sanda ta fitar a ranar Juma’a 18 ga watan FabrairuN 2022, inda su ukun suke soyayya da mata a kafafan sada zumunta ta hanyar nuna su Indiyawa ne amma ba sa zama a kasar.

Suna amfani da katinan shaidar zama ‘yan kasa na bogi tare da tabbatar wa matan cewa zasu aure su.

Kamar yadda wani SP na ‘yan sandan kasar Nipum Agarwal ya shaida cewa:

“Wadanda ake zargin suna yi wa sakarkarun mata karyar cewa hukumar da ke kulawa da shige da ficen abubuwa ta kwace kyautukan da suka tura musu daga kasar waje, don haka ana bukatar kudade don a amso.

“Ta wannan hanyar suke samun kudade inda ake tura musu asusun bankunan su.”

Farfesa Aminu Mohd Dorayi: Dan Najeriyan da ya tuka mota daga London zuwa Kano cikin kwana 24

Sanannen mai ilimin kuma dan Najeriya, mai suna Farfesa Aminu Mohammed Dorayi ya tuka motarsa mai kirar Peugeot 504 daga birnin Landan zuwa birnin Kano cikin kwanaki 24 kacal.

Dattijon ya kafa tarihi a duniya ta hanyar yin wannan namijin kokari, wajen tuka motar ta sa, inda ya yi tafiya ta tsawon mil 4,000 a cikin kwanaki 24.

Farfesa Dorayi dan tsohon dalibin jami’ar Ahmadu Bello ne dake Zaria kuma Farfesa a bangaren ilimin sinadarai.

Sannan kuma shine shugaban dalibai na jami’ar a shekarar alif 1966 zuwa 1967, Dorayi shine wanda ya shirya bangaren sharada dake jihar Kano,.kuma shine mutum na farko daya fara shirya kasuwar duniya a Najeriya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi