Idan wani dan coci na ya kuskura ya shiga shirin Big Brother, sai ya mutu, Cewar Fasto Mummy Go

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing Idan wani dan coci na ya kuskura ya shiga shirin Big Brother, sai ya mutu, Cewar Fasto Mummy Go
Idan wani dan coci na ya kuskura ya shiga shirin Big Brother, sai ya mutu, Cewar Fasto Mummy Go

Idan daya daga cikin mambobin coci na yayi kuskuren zuwa gidan big brother, sai ya mutu inji Mummy Go, LIB ta ruwaito.

Fasto mai wa’azin da ta dade tana janyo cece-kuce, Olufunmilayo Adebayo wacce akafi sani da Mummy Go, ta yi fatan mutuwa ga duk wani mamban cocin ta da ya kuskura ya shiga wasan talabijin na Big Brother Naija.

mummy go
Idan wani dan coci na ya kuskura ya shiga shirin Big Brother, sai ya mutu, Cewar Fasto Mummy Go

A cewar faston, wasan shedancin ne kuma duk wanda ke kallon wasan zai mutu.

Yayin yi wa mutanen ta wa’azi, faston ta ce:

“Duk wani mamban wannan cocin tawa da yayi kuskure ko gangancin gwada shiga wasan, zan roki Ubangiji da ya halaka shi yayin da ake tsaka da wasan.”

Daga shirin dole a zarce da shi ma’adanar gawa. Bazai sake dawowa cikin jama’a ba. Mutuwa kawai zai yi. Bazan roka mishi gafara ba. Mutuwa zan roka mishi saboda idan ya dawo, wani ma zai gwada zuwa.

Martanin Ahmed Musa ga Faston da ta ce duk ‘yan wasan kwallon kafa zasu shiga wutar jahannama

Shugaban kungiyar wasan kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa ya mayar wa wata fasto martani bayan ta ce duk wanda ya mutu a matsayin dan kwallon kafa sai ya shiga wutar jahannama.
CorrectNG sun wallafa wani bidiyo inda wata fasto ta tara jama’a tana musu wa’azi inda ta bayar da sakon mai ban mamaki.

Faston cewa ta yi duk ‘yan cocin su rubuta sakonta duk da ba za ta tilasta su su yarda da maganarta ba.
Kamar yadda tace:

“Duk wani mutum da ya mutu yana wasan kwallon kafa sai ya shiga wutar jahannama. Ku rubuta wannan, ban ce dole sai kun yarda ba, amma ku ajiye wannan a kwakwalwarku.

“Ban bukaci sai kun yarda ba. Idan danka ya zama dan kwallo ko dan’uwanka ya zama dan kwallo, ya yanki tikitin shiga wutar jahannama.”
Ganin wannan bayanin nata ne Ahmed Musa ya yi mata martani ta hanyar kara wallafa bidiyon ya yi tsokaci da “Wucewa nazo yi kawai.”
Nan da nan abokansa na kafar sada zumunta su ka fara tsokaci karkashin wallafar ida daya ya rubuta:

“Wannan wacce irin mata ce? Wannan bai yi kama da koyarwar da ke cikin Bible ba kila dai wani maganar ce ta daban.
Wani ya kara da cewa:
“Wasu suna zaune su na sauraronta, harshashashar mai wa’azin ta gama tozarta kanta.”
Wani abokin yace:
“Kalli wannan mara hankalin, wanne ne kuma tikitin shiga wuta, na yi dariya a aljanna.”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi