Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi

  • Post author:
  • Reading time:5 mins read
You are currently viewing Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi
Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi

A ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairun 2022 jarumar Kannywood, Maryam Yahaya ta saki sabbin hotunan ta a shafin ta na Instagram ba tare da ta sanya rigar mama ba.

Hotunan sun janyo mata suka da caccaka ko ta ina kafar inda wasu suka dinga zagin ta akan yadda bata dade da murmurewa daga ciwo ba ta fara shigar banza.

maryam
Sabbin hotunan Maryam Yahaya a Dubai babu rigar mama sun janyo mata zagi

Wasu sun dinga yi mata wa’azi suna cewa ya kamata ta yi wa kanta fada ta daina duk wasu ayyuka marasa kyau musamman ganin ko jikin ta bata gama mayarwa ba.

A kwanakin baya jarumar ta yi ciwo wanda mutane da dama suka zaci mutuwa zata yi don duk ta rame ta fita hayyacin.

A lokacin, masoyanta sun dinga yi mata fatan alkhairi da kuma fatan zata natsu, ciwon ya zama izina a gare ta ta gyara rayuwar ta.

Ba wannan bane karon farko da jarumar ta saba yin hotuna ba tare da ta sanya rigar mama ba. Ga masu bibiyarta a Instagram, ta kan saki bidiyoyi ko kotuna sanye da riguna da suke tabbatar da hakan.

LabarunHausa.com ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama’a:

sir_aliyuzakeey yace:

“Allah sarki Maryam Yahaya, abin tausayi a kwanakin baya. Amma yanzu lafiya ta samu shi ne kike irin wannan shiga ko tsari, duk irin shigar nan ba shi ne wayewa ba. Allah ya shirye mu gaba daya.”

Ahmad_b_ziza yace:

“Gaskiya kina rashin mutunci. Ki yi komai ba komai, aljanna ta mai rabo ce.”

akidoashiru ya ce:

“Kafa daya a duniya daya a lahira amma an ki tuba, Allah ya rufa mana asiri.”

Hajarabellohajjo2022 ta yi tsokaci da:

“Don Allah ki dinga saka bra.”

Hachim_official yace:

“Mun gani amma ki rinka saka bireziyya.”

Sir_ceeboi yace:

“Dama kin mutu kowa ya huta. In dai wannan rayuwar kika zaba toh wallahi kin halaka.”

Jaruma Maryam Yahaya ki daina wallafa bidiyoyinki, kin zama abar dariya ga makiyanki, Sayyada Sadiya Haruna

Tun bayan ciwon da Jaruma Maryam Yahaya ta yi wanda ya janyo cece-kuce sakamakon ramar da ta yi duk ta fita hayyacinta, mutane su ka tasa ta gaba.

Duk da dai jarumar ta fara wallafa bidiyoyi da hotunanta wadanda rama ta fito karara a kusan ko wacce rana, inda mabiyanta kullum su ke sukarta.

Wasu suce ta kanjame, wasu suce ta yi muni, kowa dai da irin tsokacin da yake yi akanta, sai dai babu wata jaruma ko mai fadi a ji a industiri da ta fito ta yi mata nasiha akan hakan.

A jiya, jaruma Sadiya Haruna ta yi wani bidiyo a shafinta na TikTok wanda ya yadu a kafafen sada zumunta inda ta ke yi wa jarumar nasiha.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

This Post Has One Comment

  1. Kabeer

    Allah ya kyauta Allah ya shirya mana zuri’a

Rubuta Sharhi