Yadda wani bidiyo ya nuna ‘yan sanda a Indiya na dukan mata Musulmai da suka fito yin zanga-zangar hana su sanya Hijabi

  • Post author:
  • Reading time:6 mins read
You are currently viewing Yadda wani bidiyo ya nuna ‘yan sanda a Indiya na dukan mata Musulmai da suka fito yin zanga-zangar hana su sanya Hijabi

Yayin wata zanga-zangar adawa ta dokar hana sa hijabi a Uttar Pradesh ta Ghaziabad da ke kasar Indiya an ga ‘yan sandan jihar sun farwa mata Musulmai da ke sanye da hijab da duka.

Yayin da zanga-zangar ke cigaba da gudana a wasu da ga cikin jihohin kasar a bisa kan dokar hana sa hijabi a kwalejoji, hatsaniyar ta fara ne a Karnataka wanda har ta kai ga an shiga kotu

Rundunar ‘yan sandan ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan faifan bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta inda wasu suke suka tare da caccakan ‘yan sandan.

Yan sanda sun gabatar da rahoto ga me da lamarin

Dangane da lamarin da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata, ‘yan sanda sun gabatar da rahoton farko game da bayanan abun da ya faru.

A rahoton da ‘yan sandan suka fitar, rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu labarin cewa wasu matan Musulmi kimanin su 15 dauke da takardu na nuna adawa da gwamnati sun taru a hanyar Sani Bazaar a Ghaziabad ba tare da an basu izini ba. FIR ta ruwaito cewa matan sun fara rera waka ne a lokacin da tawagar ‘yan sanda ta iso wurin.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun farma ‘yan sanda

Wasu maza da suka fito daga cikin tawagar masu zanga-zangar sun fito inda suka fara cin zarafi suna zagin jami’an ‘yan sandan da ke kokarin kora masu zanga-zangar su koma gida, a cewar FIR. A cewar korafin da ‘yan sandan su ka fitar an bayyana wani mai suna Raees a matsayin daya daga cikin wadanda ake tuhuma , kuma masu zanga-zangar sun yi barazana ga ‘yan sandan.

Yadda ‘yan sanda suka tarwatsa zanga zangar

Bidiyon ya nuna yadda ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar da karfi, kuma an hangi, wata mata sanye da niqab tana kokarin kare dukan da ‘yan sanda su ke kokarin yi mata da sanda a cikin bidiyon.

Tawagar mu ta ci karo da masu zanga-zanga mata a ranar Lahadi kimanin su 10-15 a lokacin da jami’an mu suke aikin sintiri. Sai suka tarwatsa masu zanga-zangar,” wani dan sanda a Indirapuram na Ghaziabad shine ya shaidawa manema labarai.” Ana cigaba da binciken lamarin.

Zan cigaba da fafutukar ƙwatar ‘yancin sanya Hijabi a ƙasar Indiya -Muskan Khan ɗaliba mai kishin Musulunci

Wata ɗaliba musulma mai suna Muskan Khan, wacce ta fuskanci tsangwama a wurin masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu akan hanyarta ta zuwa makaranta sanye da hijabi, a jihar Karnataka, ƙasar Indiya, ta bayyana cewa su na rera mata waka “Jai Shri Ram” saboda ta sanya hijab.

Nima sai na ce Allahu Akbar. Zan cigaba da fafutukar neman ‘yancin sanya hijab.

An samu hatsaniya sosai a jihar Karnataka ranar Talata bayan an wallafa a shafin Twitter wani bidiyon wata ɗaliba musulma sanye da hijab ta sha tsangwama a wurin masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu.

Kamar yadda aka gani a cikin bidiyon, wasu gungun maza sanye da adiko sun kewaye Muskan Khan. Sai dai ba ta karaya ba inda ta cigaba da bayyana matsayar ta. Ta faɗa cewa mafiya yawan yaran ba ‘yan makarantar ba ne.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]m

Rubuta Sharhi