29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Ina bukatar kudin raino a wurin mawaki Tekno, cewar budurwar da ta kunshi ciki daga sauraron wakar sa

LabaraiIna bukatar kudin raino a wurin mawaki Tekno, cewar budurwar da ta kunshi ciki daga sauraron wakar sa

Wata mata ‘yar kasar Zambiya ta bayyana yadda sauran wakar mawaki Tekno yayi mata sanadin daukar ciki, inda take bukatar mawakin Najeriya da ya biyata kudin rainon da, LIB ta ruwaito.

Wata mata ‘yar kasar Zambiya mai suna Rita Mwayanda ta yi korafi game da wani mawaki dan Najeriya mai suna Tekno, wadan a cewar ta sauraron wakarshi yasa ta daukar ciki.

pana
Ina bukatar kudin raino a wurin mawaki Tekno, cewar budurwar da ta kunshi ciki daga sauraron wakar sa

Mwayanda ta bayyana yadda Tekno ya saki wakar sa mai taken ‘Pana’, wacce nishadantar da ita matuka, hakan ne ya sa ta kwanta da wani mutum, wanda daga karshe ta dauki ciki. Yayin da ta nemi mawakin dan Najeriya da ya biya ta kudin daukar dawainiyar yaron.

“Dole Tekno ya biya kudin kula da dan shi. Bazan iya wahala saboda shi ba”, inji matar.

Wata mata yar kasar Zambia, ‘Rita Mwayanda’ ta bayyana wa duniya yadda mawaki dan kasar Najeriya, Tekno yayi mata sanadin haihuwar jariri, kuma yanzu haka tana dandana kudar ta.

A cewarta:


“A baya a shekarar 2016.”
“Nayi matukar son wakokin Tekno. Ina zuwa mashaya kawai domin in saurari ko wacce irin wakar sa. “A watan da ya saki wakar ‘Pana’ nayi matukar jindadi, hakan ya kai ni ga saduwa da wani mutum wanda ban sani ba, daga karshe na samu ciki. Ba don Tekno ba, da yanzu ban haifi yaron nan ba, saboda haka ina bukatar kudin daukar nauyin da daga gareshi”

Ana yada kishin-kishin mawaki Ado Gwanja ya saki matar shi Maimuna

Wani labari da muke samu marar dadin ji, akwai kishin-kishin din cewa mawaki Ado Gwanja ya saki matar shi Maimuna, inda a wani bincike da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta gudanar ta gano cewa mawakin ya sauwakewa matar tashi, kuma sakin ba daya ba har saki uku.

Tashar Tsakar Gida sun tambayi dalilin sabanin da ya haddasa sakin da tsawon lokacin da aka yi da yin sakin ba su samu wani gamsashshen bayani ba, amma dai sun tabbatar da rabuwar auren masoyan, wanda zai bakanta ran dubunnan masoyan su.

Maimuna ta cire abubuwan da suka shafi Ado Gwanja a shafinta

Haka kuma a wani bincike da Tashar Tsakar Gida ta sake gudanarwa a shafin Maimuna, sun gano cewa ta cire duk wani abu da ya shafi Ado Gwanja a shafinta, hatta sunan Ms Ado Gwanja da ta sa ta cire ta sa sunan “Fashion Beauty”, haka shafin da take kasuwancin ta mai suna “Munat Gwanja Collection” shi ma ta canja shi zuwa “Munat Dan’auta Collection”.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe