Hukumar kwastam ta samu nasarar kwace katan 383 na maganin kara karfin maza yayin jima’i iri-iri

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing Hukumar kwastam ta samu nasarar kwace katan 383 na maganin kara karfin maza yayin jima’i iri-iri
Hukumar kwastam ta samu nasarar kwace katan 383 na maganin kara karfin maza yayin jima’i iri-iri

Hukumar kwastam mai dakile fasakwabrin kayayyaki a Najeriya ta bayyana yadda ta kama maganin tari na codeine wanda yakai darajar naira miliyan 212 da kuma maganin karin kuzarin ga namija yayin saduwa BBC Hausa ta ruwaito.

Hammi Swomen, shugaban hukumar kwastam na yankin Apapa da ke jihar Legas, ya ce sun kama kwantena dauke da katan guda 2,875 na maganin tarin da kuma kanta guda 383 na kwayoyin dake kara wa maza kuzari yayin saduwa, wadanda aka bayyana sunayen su daban-daban.

fasa kauri 1
Hukumar kwastam ta samu nasarar kwace katan 383 na maganin kara karfin maza yayin jima’i iri-iri

Haka zalika, an samu katan guda 99 na injin mai nima abubuwa daban-daban a cikin kwantenar.

“Mun samu bayani akan yadda aka dauko flas din abinci, amma kamar yadda kike gani ya bayyana abubuwa ne da suka bambanta gaba daya,” a cewarsa.

Ya cigaba da bayyana cewa “wannan ba kage bane, kawai an shigo da haramtattun kaya ne”.

A halattawa maza su dinga mallakar baiwa da za su ke jima’i da ita – Salwa Al-Mutairi

Dole za ku yi mamaki kan abinda wannan rahoto yake magana, amma muna tabbatar muku ba kage bane muka yi. Wannan magana ta fito daga bakin fitaciyyar ‘yar siyasa dake kasar Kuwait. Mu kawai muna rubuta abinda ta fada ne a wani bidiyon ta.

Wani ya sanar dani cewa mahaifin shi ya bashi kyautar baiwa da zai ke yin jima’i da ita, ya kuma ce zai tarairayeta yadda ya kamata, haka kuma ya ce mallakar baiwa ya halatta a Musulunci. Wannan labari ya tunatar dani wani lamari da ya faru dani shekara 2 da suka wuce, lokacin dana yi aiki da shi yana matukar son mata.

A lokacin ina matukar jin tausayin sa, haka kuma ina ta kokari akan aikina. Haka ya sanya na fara zuwa wajen Malaman Addini domin neman shawarar su akan wannan matashin saurayi. Na tambayesu akan halaccin mallakar mace baiwa

Sun bayyana cewa hanyar da za a samu baiwa mace shine, idan kasar Musulmai sun kai yaki kasar da ba Musulmai ba sai suka samu nasara suka kama bayi. Sai na tambayesu hakan ya halatta?

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Rubuta Sharhi