Manta da batun iya girki ki nemi kudi, yanzu maza mata masu kudi suke aure, shawarar wata mata ga ‘yan mata

  • Post author:
  • Reading time:4 mins read
You are currently viewing Manta da batun iya girki ki nemi kudi, yanzu maza mata masu kudi suke aure, shawarar wata mata ga ‘yan mata
Manta da batun iya girki ki nemi kudi, yanzu maza mata masu kudi suke aure, shawarar wata mata ga 'yan mata

Wata mata ta janyo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Twitter bayan ta bayyana cewa yanzu maza mata masu kudi suke so. Ta ce matsawar girki kadai mace ta iya, zata mutu ba aure.

Jenny ta ja hankalin mata akan jajircewa wurin neman kudi maimakon su tsaya suna koyon girke-girke.

Wallafar ta ta ja janyo cece-kuce a Twitter inda wasu suka yarda da maganar ta sannan wasu suka musanta.

WhatsApp Image 2022 02 11 at 19.17.12

Kamar yadda ta wallafa:

“Yanzu maza mata masu kudi suke so. Zaki mutu babu aure idan girki kadai kika iya ‘yar uwata.”

Wasu maza sun yaba da wallafar har suke cewa sun fi son su auri mace mai kudi ko da kuwa bata iya girki ba.

Wasu mabiyanta kuwa cewa suka yi akwai mazan da har yanzu mata wacce zata gyara musu gida ta kuma yi musu girki suke so.

Yawancin matan da suka ga wallafar sun ki amincewa da wallafar, inda suka ce ba gaskiya bane, babu kuma bukatar mace ta dage wurin neman kudi.

‘Yan sanda sun cafke wasu matasan da suka kashe budurwar domin yin tsafin kudi da ita

Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu matasa uku da laifin kashe wata budurwa domin yin tsafin kudi da ita a jihar Ogun

An kama su ne bayan wani jami’in tsaro ya gansu suna kona wani abu da ake tuhuma wanda ya zama kan mutum a cikin wata tukunya

A halin yanzu, jami’an ‘yan sanda na ci gaba da neman mutum na hudu wanda ake zargi da zama saurayin wacce aka kashe
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wasu matasa hudu da laifin kashe budurwar daya daga cikin matasan saboda su yi tsafin kudi da ita.

A cewar sanarwar da Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ‘yan sandan suka samu a ranar Asabar din da ta gabata a hedikwatar yankin Adatan daga hannun shugaban jami’an tsaro na al’umma, cewa an ga wadanda ake zargin suna kona kan mutum a cikin tukunya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: [email protected]

Rubuta Sharhi