27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi ya zama mutum na farko a duniya da ya samu masoya miliyan 400 a shafin Instagram

LabaraiCristiano Ronaldo ya kafa tarihi ya zama mutum na farko a duniya da ya samu masoya miliyan 400 a shafin Instagram

Ɗan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo, ya saba kafa sabon tarihi a cikin filin wasa, sai dai yanzu ɗan wasan ba’a nan kawai ya ke kafa sabon tarihi ba.

Cristiano Ronaldo mai shekaru 37 a duniya ya zarce mabiya miliyan 400 a shafin Instagram inda ya zama mutum na farko da ya taɓa yin hakan a duniya.


Cristiano Ronaldo
Ɗan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo. Hoto daga Instagram @cristiano

A cikin watan Satumban 2021, ɗan wasan ya na da mabiya miliyan 237 a shafin inda ya zama wanda ya fi kowa mabiya a manhajar. Tun daga wannan lokacin mabiyan sa sun cigaba da ƙaruwa sosai a cikin watanni kaɗan.

A cikin wallafa 3242 da yayi, ya samu a ƙarance ‘likes’ miliyan 10. Ronaldo yana bin mutane 500 ne kawai a shafin.

Cristiano Ronaldo ya nuna godiyar sa ga masoyan sa

Ronaldo, wanda yayi murnar zagayowar ranar haihuwar sa cikin yan kwanakinnan, ya godewa masoyan sa bisa ɗumbin fatan alkhairin da su ka yi masa a kafar ta sada zumunta.

Rayuwa faɗi tashi ce. Aiki tukuru, Jajircewa, nuna ƙwazo da neman fata. Amma a ƙarshe, iyali, ƙauna, gaskiya, da abota su ne abin da ya daraja ta. Nagode da saƙonnin ku! Shekaru 37 zamu cigaba da ƙirgawa. Dan wasan ya rubuta a shafin sa na Instagram

Kylie Jenner ita ce ta zo a matsayi na biyu cikin masu yawan mabiya inda ta ke da mabiya miliyan 308 a shafin na Instagram. Lionel Messi yana a matsayi na uku da mabiya miliyan 306.

Ɗan wasan yasha yabo

Shahararren mai watsa shirye-shirye, Piers Morgan, ya wallafa wani hoton sa tare da Cristiano Ronaldo a shafin Twitter. Inda ya rubuta cewa:

Ina taya ka murnar zama mutum na farko da ya samu mabiya miliyan 400 a Instagram. Babban sarkin kafafen sada zumunta wanda ba kamar sa. Mutum 500 kawai ya ke bi a shafin wanda ya haɗa da ni. Ya san rubutu mai kyau idan ya ci karo da shi.

Dalilai 3 da ya sanya Musulmai ke son Cristiano Ronaldo

An yabawa shahararren dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo, bayan ya dauke kwalbar lemo na Coca-Cola da aka ajiye a gaban shi a lokacin wata hira da aka yi dashi a shekarar 2020.

Ya bukaci mutane su sha ruwa maimakon Coca-Cola, yayin da ya rike robar ruwa a hannunshi, ya daga sama ya kira kalmar “Agua” da yaren Portugal, ma’ana ruwa kenan.

Ronaldo kowa ya san shi da iya magana, ba wai iya kwallo kawai ya iya bugawa ba, ya kasance mutum mai kulawa ga al’umma hakan ya sanya ya zama daban da sauran ‘yan wasa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe