27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

2023: Har yanzu ina da kuzarin sake tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna, cewar Isah Ashiru

Labarai2023: Har yanzu ina da kuzarin sake tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna, cewar Isah Ashiru

Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a zaɓen 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Hon Isa Kudan Ashiru, ya ce har yanzu yana nan daram zai sake tsayawa takara a zaben gwamna na 2023 a jihar domin samar da ribar dimokuraɗiyya ga al’ummar mazabar sa.

Ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da wasu abokan sa na siyasa a jihar a ranar Alhamis.

Ashiru wanda ya ce ya lashe zaben gwamna a 2019, amma an tabka magudi, ya ce a zaɓen 2023 ba zai bar komai ba kuma ya bi hanyoyin da suka dace don samun nasara.

Ya jaddada cewa har yanzu burinsa na yin mulkin jihar Kaduna a jam’iyyar PDP yana nan daram.

” Ina da niyyar ci gaba har sai an samu nasara,” in ji shi.”

Ku tuna cewa Ashiru yayi wa’adi biyu a majalisar dokokin jihar Kaduna inda ya wuce majalisar wakilai inda kuma ya sake yin wa’adi biyu.

Ya yi takara da Gwamna Nasir el-Rufai a jam’iyyar All Progressives Congress a shekarar 2015 kuma ya sha kaye a zaɓen fidda gwani kafin ya koma PDP kafin zaɓen 2019.

Ya zama dan takarar gwamna a PDP amma El-Rufai ya doke shi.

Ashiru ya ce, “Abin sha’awa ne. A siyasa idan aka yi rashin nasara a karon farko ba asara ba ce. Wannan wasan ba game da ni bane, game da mutanena ne. Ina da hangen nesa wanda na yi imani idan aka ba ni dama, zan canza rayuwar jama’a ta zuwa mafi kyau.

“Don haka, ban shiga siyasa in yi wa kaina hidima ba amma don in yi wa jama’ata hidima. Abubuwa sun canza. Ina jin ina da wani abin da ya fi dacewa da zan bayar don inganta tattalin arziki da zamantakewar jama’armu shi ya sa zan sake tsayawa takara .”

Dan takarar gwamnan ya yi alkawarin sanya kwamitin yaƙin neman zaɓen nasa ya zama mai dunƙulewa tare da yin shawarwari sosai.

Wata sabuwa: Ƴan majalisa na yunƙurin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara, sun fara shirye-shiryen tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Gusau daga muƙamin sa.

Wannan ya biyo bayan bayyana ƙudirin tsige mataimakin gwamnan a gaban shugabannin majalisar.

Mataimakin kakakin majalisar, Musa Bawa ya miƙa takardun a hannun kakakin majalisar, Nasiru Mu’azu, ranar Juma’a a harabar majalisar da ke a babban birnin jihar Gusau.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe