29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Sai da aka ce dole sai na cire Hijabi na idan har ina son na yi suna a duniya -Shatu Garko

LabaraiSai da aka ce dole sai na cire Hijabi na idan har ina son na yi suna a duniya -Shatu Garko

Shatu Garko wacce ta lashe kambun sarauniyar kyau ta Najeriya ta bayyana ƙalubalen da ta fuskanta a matsayin ta na mace mai sanya hijabi.

Shatu Garko
Shatu Garko, sarauniyar kyau ta Najeriya.

Shatu Garko mai shekaru 18, wacce ta lashe gasar ta karo na 44, ta zama mace ta farko mai sanye da hijabi da ta lashe gasar inda ta buge sauran mutum 18, ta bayyana hakan ne a yayin wata zantawa da jaridar PUNCH.

Shatu Garko ta fuskanci ƙalubale sosai a farko

Shatu Garko ta bayyana cewa da farko ta sha ƙalubale sosai saboda hijabin ta.

A cewar ta, kamfanunnika da dama sun ƙi yin aiki da ita a saboda ta na sanya hijabi inda su ke shawartar ta da sai ta cire hijabi idan har tana son ta samu nasara a sana’ar tallan kayan ƙawa.

Ban kai shekara ɗaya ba da zama mai tallan kayan ƙawa. Bayan na kammala makaranta, na zauna a gida saboda annobar cutar korona. Na tsani zama hakanan bana yin komai, sai na yanke shawarar na gwada sa’a ta a harkar tallar kayan ƙawa.

Na sha wahala a gwajin farko da nayi. Da farko sun ɗauke ni amma daga baya su ka faɗa min cewa ina bukatar samun gudanarwa mai kyau, inda su ka ƙi yin aiki da ni.

Guiwoyin ta ba su sare ba

Sai dai hakan bai sanya guiwoyina sarewa ba, amma ya ƙara min ƙarin ƙarfin guiwar ƙara dagewa sosai.

Mahaifiyata ta bayyana min cewa, “ba daga farawa kawai zaki samu nasara ba”. Ta sanya na fahimci cewa dole sai mutum ya faɗi kafin ya samu nasara.

A farkon fara wannan sana’ar tawa, na sha wahala saboda hijabi na. Kamfanunnika da dama sun ƙi bani damar aiki da su. A lokuta da dama an faɗa min cewa sai na cire hijabi na idan ina son nayi nasara a matsayin mai tallar kayan ƙawa.

Mahaifina ya shiga damuwa, a tunaninsa za a ware ni saboda hijabi na, Shatu Garko

Shatu Garko, wacce ta lashe gasar sarauniyar kyaun Najeriya ta 44 ta bayyana yadda ta samu mahaifinta ya amince ta shiga gasar.

Budurwar mai shekaru 17 ta zama mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar inda ta zama sarauniyar kyau ta Najeriya tun da aka kirkiri gasar a shekarar 1957, The Punch ta ruwaito.

A cewarta:

“Mahaifiyata ta fi kowa ba ni kwarin guiwar shiga gasar inda tace ba wani abu mai wahala bane. Sai dai mahaifina ba wani so yayi ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe