27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Nazir ka keta mutuncin mu, kuma ka keta mutuncin masana’antar mu ta Kannywood – Abubakar Bashir Mai Shadda

LabaraiKannywoodNazir ka keta mutuncin mu, kuma ka keta mutuncin masana'antar mu ta Kannywood - Abubakar Bashir Mai Shadda

A yayin da Daraktoci da Furodusoshi suka yi caa akan jaruma Ladi Cima suna yi mata raddi a maganar ta, wacce ta bayyanawa BBC Hausa cewa ba a taba bata kudin da ya wuce dubu biyar ba a duk shekarun da ta kwashe tana fitowa a cikin fina-finan Kannywood.

Fitaccen Mawakin nan Nazir M Ahmad ya fito ya goyi bayan ta, inda maganar shi tafi karfi kan jarumi Ali Nuhu da Falalu A Dorayi, da suka fito suka ce suna bawa jarumar kudade masu kauri a duk lokacin da suka sanya ta a fim.

Maganar Nazir ba ta yiwa ‘yan Kannywood dadi ba

To sai dai kuma maganar ta Nazir ba a nan ta tsaya ba, domin kuwa ya bayyana cewa shi da kanshi shaida ne akan abubuwan dake faruwa a masana’anatar, inda har ya bayyana cewa wannan dalili na zulunci shine yasa ake samun koma baya a masana’antar.

Haka kuma Nazir Sarkin waka ya bayyana cewa wasu ma sune suke cire kudi a aljihunsu su biya domin a saka su a fim, ko kuma idan mace ce, sai ta bada jikinta an kwanta da ita kafin a saka ta a cikin fim.

Nazir M Ahmad (Sarkin Waka)
Nazir M Ahmad (Sarkin Waka) – Hoto: Instagram – sarkin_wakar_san_kano

To sai dai kuma wannan magana ta Nazir ba ta yiwa da yawa daga cikin jarumai da daraktocin na Kannywood ba, domin kuwa bai jima da sakin wannan bidiyo na shi ba, fitaccen daraktan nan Abubakar Bashir Mai Shadda ya fito yayi masa martani a wani bidiyo.

Ga Abinda yake cewa

“Assalamu Alaikum Warahamatullahi Ta’allah Wabarakatuhu, masoyanmu a duk inda suke a fadin duniya, da kuma kai Naziru Mawakin tsohon Sarkin Kano, wanda ya kamata na fito na baka amsa, akan maganganun da kayi a Instagram.

“Ba na yin irin wannan bidiyon, ban kuma taba yi ba, amma yau ina so nayi saboda ka keta mutuncin mu, ko kuma na ce ka keta mutuncin masana’antar mu, wanda dole sai mun fito mun baka amsa a cikinta.

“Allah yana gani, maganar da Mama Tambaya tayi na cewa ba a taba bata kudi sama da dubu biyu ko sama da dubu biyar ba, wannan magana ba haka take ba, za a iya yiwa Mama Tambaya uziri na duba da shekarunta, amma ita ma ta san cewa mutane da yawa a cikin masana’antar sun bata sama da wannan kudin, a ciki har da ni Abubakar Bashir Mai Shadda, akwai Ali Nuhu, akwai Falalu A Dorayi, akwai sauran furodusoshi da suka yi magana kan wannan abu.

“Mu a masana’antar Kannywood babu wani mutum da ya taba yi mana aiki bamu biya shi hakkin shi ba, idan kuma akwai wanda yayi mana aiki bamu biya shi ba, sai ya fito ya fada.

“Ka fito kana ta wasu surutai, kana fadar maganganu na iska, to ka gane cewa duk abinda ka fada zamu iya mayar maka da martani, saboda ba tsoronka muke ji ba, kuma baka isa ka fito ka ci mutuncin masana’antarmu mu rabu da kai ba.

Ba mu da abinda ya kai masana’antar Kannywood

“Wannan masana’antar bamu da abinda ya kai ta, kuma kai ma dan cikin masana’antar nan ne, wannan masana’antar ita tayi maka riga, ita tayi maka duk abinda kake takama dashi.

“Idan magana ce ta ana aiki ba a biyan mutane kai ya kamata a tambaya wannan mu bamu san wannan ba, saboda mu bama yi, a ayyukan mu da muke yi bama, idan kuma akwai wanda muka yiwa ya fito ya fada cewa mun rike masa hakkinsa.

“Dan Allah idan kana soki burutsunka, ka dinga sanin abinda zaka dinga fadi, ka daina sako masana’antar mu, saboda Wallahi duk lokacin da zaka yi irin wannan sai mun fito mun baka amsa, saboda mun ga kamar kana nema ka taba mutunci da martabar masana’antar mu.

Wallahi abinda tsohuwa ta fada gaskiya ne, wasu matan ma sai an kwanta da su ake sa su a fim – Sarkin Waka

Fitaccen mawaki kuma jarumi a masana’antar ta Kannywood, Nazir M Ahmed wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya fito ya goyi bayan Ladi Cima, inda ya tabbatar da cewa wannan magana da ta fada haka take babu ja.

Sarkin Waka ya kawo hujjoji da dama wadanda yayi amfani da su ya kare maganganunsa da su, inda har rantsuwa yayi da Allah cewa wannan magana da tayi gaskiya ce, idan kuma har akwai wanda yake da ja ya fito ya ja.

A wani bidiyo da yayi mai tsawon minti 6 da dakika 46, wanda ya wallafa a shafinsa na Instagram, jarumin ya yi magana cikin bacin rai, kan yadda jaruman na Kannywood suka sako tsohuwar a gaba suna neman sanya mata hawan jini.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe