29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wallahi abinda tsohuwa ta fada gaskiya ne, wasu matan ma sai an kwanta da su ake sa su a fim – Sarkin Waka

LabaraiKannywoodWallahi abinda tsohuwa ta fada gaskiya ne, wasu matan ma sai an kwanta da su ake sa su a fim - Sarkin Waka

A yayin da hirar da BBC Hausa ta yi da Ladi Cima take cigaba da tada kura a shafukan sada zumunta Daraktoci da yawa sun fito suna kare kan su tare da bayyana hujjoji da kuma irin abin akhairin da suka yiwa dattijuwar.

Sai dai kuma shi a nashi bangaren fitaccen mawaki kuma jarumi a masana’antar ta Kannywood, Nazir M Ahmed wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya fito ya goyi bayan Ladi Cima, inda ya tabbatar da cewa wannan magana da ta fada haka take babu ja.

Sarkin Waka ya kawo hujjoji da dama wadanda yayi amfani da su ya kare maganganunsa da su, inda har rantsuwa yayi da Allah cewa wannan magana da tayi gaskiya ce, idan kuma har akwai wanda yake da ja ya fito ya ja.

A wani bidiyo da yayi mai tsawon minti 6 da dakika 46, wanda ya wallafa a shafinsa na Instagram, jarumin ya yi magana cikin bacin rai, kan yadda jaruman na Kannywood suka sako tsohuwar a gaba suna neman sanya mata hawan jini.

Jaruma Ladi Cima
Jaruma Ladi Cima – Hoto: BBC Hausa

Ga dai abinda Sarkin Waka yake cewa kan maganar ta Ladi Cima

“Assalamu Alaikum jama’a, wato ayi hakuri, ina jin kamar shi ba bacin rai ba, bacin rai haka nake, wannan magana ta Ladi ni yanzun nan nake haduwa da ita a shafukan sadarwa. Gaskiyar magana ‘yan fim babu Allah a ranku.

“Duka mutanen da suka yi magana akan matar nan Wallahi babu Allah a ranku, yanzu kamar Ali Nuhu da Falalu A Dorayi, dan Allah kune za ku ce baku san ana yiwa dattijan nan wannan abin ba, su tashi aiki a dauki dubu biyu ko dubu daya ko kuma a ce za a kira su. Haba mu ji tsoron Allah mana, kun san ana yi.

“Yanzu bari na fara da Falalu A Dorayi, matar nan fim nawa tayi a masana’anta? Matar nan tayi fim yafi a kirga, fim nawa ne ka saka ta har zaka karyata maganarta don ta ce dubu biyu, dubu hudu ake ba ta?

“Ai a tayi fim ya kai 20, to ya kamata a ce sai fim 18 sun biya ta wannan kudi, shine idan tayi maganar ba ta yi daidai ba. Darakta mu yi maganar gaskiya mana, mu daku mun san akwai yaran da za ka zo ka saka mutum yayi maka furodusa, zai dinga cutar mutane, bama kokari mu dinga biyan su da kan mu, mun san da wannan.

“Ko kuma shi Ali Nuhu, fim nawa ne ya saka ta a ciki, nawa ne ya bata 40,000? Mun sani ba karya bane ba, kwanan nan anyi wannan, na kira tsofaffi su fito a fim, ina tambaya nawa ake biyansu aka ce dubu biyu. Na kira wata ta fito a fim ta gama an dauki kudi an bata, ana bata kudin naga kamar tayi sujjada, na ce nawa ake biyan su, da bakinta ta fada, kuma na bincika naga hakane.

Ku bar tsohuwa ta zauna lafiya

“Mun san wannan magana, ku bar tsohuwa ta zauna lafiya, ba wai iya tsofaffi kawai ake yiwa ba, duk wanda za a saka a fim, in dai ba babban jarumi bane, sai dai a bashi dubu biyu, dubu uku, shi yasa harkar take ta yin kasa. Kawai idan kuna da niyyar ku gyara ku fito ku gyara, idan kun kawo jarumi ku biya shi da kan ku.

“Ni na san fina-finan da ba ma biyan mutum ake yi ba idan ya fito, shine yake biya, kuma kun san da wannan kuma, yanzu wannan tsohuwar da aka sako a gaba so kuke hankalinta ya tashi wani abu ya same ta daban.

“Na rantse da Allah da ya halicce ni, in kuma wani ya isa ya fito ya ce ba haka ake wannan zaluncin ba, Wallahi haka ake yi, wasu ma tura su za ayi ace za ayi musu waya, wasu kuma sai sun biya kudi, ko kuma sun bada wani abu makamancin kudi, ko ki bada kudi, ko kuma ki bada kan ki, ba sune abubuwan da ake fama da su ba?

Abinda ya kamata kuyi yanzu shine ku gyara

“Idan kun ce wasu ne ake wakiltawa suke zaluntar wasu na yadda, ko wasu ne suke cin kudin wasu na yadda, ku kuce ba ku bane, amma maganar tsohuwar nan gaskiya ne.

“Abinda ya kamata kuyi shine ku gyara ku mika sakon da zaku bawa mutum tsakaninku da shi, kuma idan kunga baku da kudi kada a dauko fim, a bari sai ana da kudi a dauko shi. Amma na rantse da Allah ana biyansu hakaa, ko kuma wani a cikin ku da kuka yi magana ya fito ya rantse ya ce ba a biyansu haka.

“Duk wadanda suke kiran kansu manya a masana’antar nan ba lissafi ne suke na yadda za ayi masana’anta ta ci gaba ba, lissafi ne na yadda su za su samu cigaba.

Ga dai bidiyon maganar ta shi a kasa:

Kotu ta bada umarnin a kamo mata jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana

A wani labari da muka ci karo dashi da jaridar Freedom Radio ta wallaafa, ya nuna cewa wata kotu a jihar Kano ta bada umarnin a kamo mata fitaccen jarumin kamfanin fina-finan Hausa na Kannywood, Sadiq Sani Sadiq.

Kotun ta shari’ar Musulunci dake zama a unguwar Hotoro, karkashin jagorancin Mai Shari’a Sagir Adamu ita ce ta bada umarnin Kamo Sadiq Sani Sadiq, sakamakon bijirewa umarninta da yayi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe