34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Jami’ar Ulamat ta bawa Muskan kyautar N5m kan jarumtar da tayi na tunkarar ‘yan addinin Hindu tana kiran Allahu Akbar

LabaraiJami'ar Ulamat ta bawa Muskan kyautar N5m kan jarumtar da tayi na tunkarar 'yan addinin Hindu tana kiran Allahu Akbar

Jami’ar Ulamat dake kasar Indiya ta bawa ‘yar gwagwarmaya Muskan Khan kyautar naira miliyan biyar (N5m) kan jarumtar da ta nuna wajen tunkarar mabiya addinin Hindu tana kiran Allahu Akbar.

Jami’ar Ulema-e-Hind ta sanar da bayar da tukuicin Naira miliyan 5 ga dalibar da ta iya fitowa sanye da Nikab ta tsaya a gaban taron samari ta ce Allahu Akbar ‘Jai Shri Ram’ a garin Karnataka. Jami’ar ta ce za ba da tukwicin ga dalibar wacce ta nuna wannan bajinta.

Faifan Bidiyo

A wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta na yanar gizo, adadin mutanen da suka fito domin nuna goyon bayansu ga dalibar da ta dinga kiran Allahu Akbar a gaban jama’a ya karu sosai.

Jami’ar Ulema karkashin jagorancin IMIM Chief Hyderabad MP Asaduddin Owaisi- ta sanar da bayar da tukuicin 5,000,000 ga yarinyar da tayi wannan jarumta.

An fitar da takarda dauke da sa hannu

An fitar da takarda a karkashin goyon bayan shugaban inda ya rubuta cewa dalibar ‘yar jami’ar PES College Mandya, Bibi Muskan Khan, diya ga Muhammad Hussain Khan, wadda ta yi jarumtar shiga gaba a zanga zangar da ta gudana na neman hakkinta akan addini, ta samu kyauta da ga Jami’ar Ulema-e-Hind.

Mun Taya Hazrat Maulana Mahmood Asad Madani murna, tare da yi mata fatan alherin samun cigaba a rayuwa. Jami’ar Ulema-e-Hind ta sanar da bayar da tukuicin kudi har naira miliyan 5 saboda karfafa wa wannan jarumar gwiwa.

Muskan Khan
‘Yar Gwagwarmaya Muskan Khan

Wacece Muskan Khan?

Muskan, daliba ce ‘yar aji biyu a fannin na’ura mai kwakwalwa a kwalejin PES da ke Mandya, ta fuskanci taron jama’a inda take kwarototo wanda hakan ne ya sanya ta zama abun kasawa a faifai.

Hirar ta da Indian Express

Da take zantawa da Indian Express dalibar ta ce a jami’ar da take karatu an ba ta damar sanya Nikab da hijabi a aji. Ta ce:

“Hukumar jami’ar da kuma shugaban makaratar ba su hana ni saka Nikab di na ba. Sai Wasu daga waje suke zuwa suna takura mana, su waye wadannan da za su zo su hana mu? Me ya sa za mu saurare su?

Yadda lamarin ya faru

Da take magana a kan ranar da lamarin ya bayyana a faifan bidiyo, Muskan ta ce:

“Na kama hanyar makaranta zan je na kai aikin da aka bamu, tun kafin in shiga jami’a na ga wasu ‘yan matan Musulmai ana cin zarafin su akan sun saka hijabi, suna kuka.

“Na zo nan ne dan in yi karatu, kwalejin da nake ta ba ni damar saka waɗannan kayan. Kashi 10% ne kawai na ɗaliban suke makarantan mu, sauran yan wasu makaran ta ne. Yadda naga sunayi sai abun ya dame ni har na tsoma baki “

A cikin faifan bidiyon, an ga shugabar kwalejin da sauran ma’aikatan na kokarin shawo kan lamarin.

Muskaan ta ce:

Da na isa aji sai shugaban makarantar mu ya tsaya kusa da ni ya ce ‘Na barki ki kisa niqab dinki kar ki damu, an kuma amince mu saka har cikin aji.

Har ya zuwa yanzu babu wanda ya sami wata matsala a jami’ar, kwanaki biyu da suka wuce ne wasu daga waje suka fara kawo wannan matsalar.

Zan cigaba da fafutukar ƙwatar ‘yancin sanya Hijabi a ƙasar Indiya -Muskan Khan ɗaliba mai kishin Musulunci

An samu hatsaniya sosai a jihar Karnataka ranar Talata bayan an wallafa a shafin Twitter wani bidiyon wata ɗaliba musulma sanye da hijab ta sha tsangwama a wurin masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu.

Kamar yadda aka gani a cikin bidiyon, wasu gungun maza sanye da adiko sun kewaye Muskan Khan. Sai dai ba ta karaya ba inda ta cigaba da bayyana matsayar ta. Ta faɗa cewa mafiya yawan yaran ba ‘yan makarantar ba ne.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarnhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe