27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yan ta’adda sun halaka mutum 7, sun lalata gada daya tilo da za’a bi a kai musu hari a jihar Kaduna

Labarai'Yan ta'adda sun halaka mutum 7, sun lalata gada daya tilo da za'a bi a kai musu hari a jihar Kaduna

An halaka kusan mutum bakwai a ranar Talata lokacin da ‘yan ta’adda su ka kai farmaki a wasu ƙauyuka guda uku a ƙaramar hukumar Zangon Kataf cikin jihar Kaduna.

Mai magana da yawun ƙungiyar The Southern Kaduna Peoples Union Public, Mr Luka Binniya, ya tabbatar wa jaridar PUNCH da aukuwar lamarin ranar Laraba.

A cewar sa, ‘yan ta’addan sun ƙona gidaje da dama sannan su ka halaka mutum ɗaya a ƙauyen Zaman Dabo, yayin da aka halaka wasu mutum shida a ƙauyukan Chibob da Sabon Kaura.

‘Yan ta’addan sun buɗe wa mutane wuta

Binniya ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun farmaki ƙauyukan ne cikin gungu mai yawa sannan su ka buɗe wa mazaunan ƙauyukan wuta, inda su ka lalata dukiya mai ɗumbin yawa.

Ƴan ta’addan sun yi amfani da rashin jami’an tsaro a safiyar ranar Talata tsakanin Unguwar Wakili da Abuyab inda su ka lalata gada ɗaya tilo da ta haɗa ƙauyukan biyu.

'yan ta'adda sun lalata gada
Gadar da ‘yan ta’addan su ka lalata. Hoto daga jaridar Punch

Yanzu haka da na ke magana da kai, ko babur ba zai iya wucewa ta wannan gadar ba. Ya kamata ayi gaggawar gyara wannan gadar saboda mutanen waɗannan ƙauyukan na cikin fargabar waɗannan ‘yan ta’addan.

Ba a samu jin ta bakin hukumar ƴan sanda ba

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran da aka yiwa wayar sa ba a lokacin haɗa wannan rahoton.

Yan bindiga sun sace wata mata tare da ɗiyarta a jihar Bauchi

Waɗansu ‘yan bindiga sun sace wata mata, Khadija Audu-Ardo, mai shekaru 40 a ƙauyen Tsamiya na yankin Boi, a ƙaramar hukar Bogoro, jihar Bauchi. Jaridar PUNCH ta ruwaito.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’an tsaron haɗin guiwa da ke a yankin Boi, ƙaramar hukumar Bogoro, su ka ba ‘yan jarida ranar Talata a Bauchi.

A cewar sanarwar, matar an ɗauke ta ne tare da ɗiyar ta zuwa wani wuri da ba’asan ko ina ba ne a daren ranar Litinin.

Da misalin ƙarfe 12 na dare, mazauna ƙauyen sun kawo mana rahoton sace Khadija Audu Ardo wanda wasu mutane ɗauke da manyan bindigu su kayi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe