27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Al’ummar Najeriya sun zama wani abu daban idan har Malamai za su zama masu cin amana – Aisha Buhari

LabaraiAl'ummar Najeriya sun zama wani abu daban idan har Malamai za su zama masu cin amana - Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari, ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da adalci ga Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara biyar da malaminta Abdulmalik Tanko ya yi garkuwa da ita kuma daga bisani ya hallaka ta…

Aisha Buhari ta yi wannan kiran ne a gidan gwamnati jihar Kano a ranar Laraba lokacin da ta ziyarci jihar kan ziyarar ta’aziyyar rasuwar Hanifa da kuma babban Malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ahmad Bamba.

Uwargidan shugaban kasar ta samu tarba ne daga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da mai dakinsa Hafsat Ganduje.

Da take jawabi a gidan gwamnati, Aisha Buhari ta bayyana cewa babban makasudin zuwanta Kano shi ne tazo ta yi ta’aziyya ga gwamnatin jihar Kano. Da kuma iyalai da al’ummar jihar bisa rasuwar Sheikh Ahmad Bamba da kuma jajantawa iyayen Hanifa bisa mumunan kisan da aka yi mata.

Matar shugaban kasa Aisha Buhari
Matar shugaban kasa Aisha Buhari

Ta nuna bakin cikinta kan yadda Malamin Hanifa ya ci amanar iyayenta ya sace ta da ga bisani kuma ya hallaka ta.

A cewar Aisha Buhari, idan malami zai iya rufe ido ya ya ci amanar yarda da ke tsakaninsa da dalibai da iyayensu, to fa “al’umma ta zama wani abu dabam.”

Ina da ‘ya’ya da jikoki, jikoki na suna makaranta kuma ina ganin yadda suke daura yarda da amana akan malamansu.

“Idan malamai za su dinga keta wannan amana, to fa al’ummarmu ta zama wani abu dabam,” in ji ta.

Uwargidan shugaban kasar ta kuma yabawa Gwamna Ganduje kan kudirinsa na tabbatar da anyi adalci ga marigayiya Hanifa, tana mai cewa dole ne a yi adalci domin ya zama darasi ga sauran mutane.

Sannan kuma ta jajantawa al’ummar jihar Kano bisa wannan mummunan lamari da ya afku, kamar yadda ta jajantawa gwamnati da iyalan marigayi Sheikh Bamba bisa rasuwarsa.

Daga nan sai uwargidan shugaban kasar ta yi addua ga Allah Madaukakin Sarki da ya jikan su ya kuma baiwa iyalansu hakurin jure rashin.

A cikin jawabin nasa, Gwamna Abdullahi Ganduje ya kuma koka da yadda wanda alhakin kula da ita ya rataya akansa shine ya kashe ta.

Wannan abin takaici ne. Zamu tabbatar da anyi adalci akan kisan Hanifa domin ya zama izina ga sauran masu tunanin aikata makamancin wannan danyen aikin.

“Bari in tabbatar muku ba zan bata ko dakika daya wajen ganin na yi abunda dokar tsarin mulkin kasa ta tsara ga wanda aka gurfanar ake tuhuma a gaban kuliya. Ina mai tabbatar muku da cewa za mu bi hakkin yarinyar da bataji bata gani ba. ‘yar mu ce dole mu yi mata adalci,” in ji Ganduje.

Muna goyon bayan hukuncin Malam – Aisha Buhari ta goyi bayan Sheikh Abdallah kan a yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta sanya baki dangane da maganar hukuncin da ya kamata a yankewa Abdulmalik Muhammad Tanko, shugaban makarantar su Hanifa Abubakar, wacce ya sace ta ya kuma yi mata kisan gilla.

Matar shugaban kasar ta bayyana ra’ayinta a shafin ta na Instagram a ranar Litinin 24 ga watan Janairu, inda ta nuna goyon bayan ta akan a kashe Abdulmalik Tanko kamar yadda ya dauki rayuwar Hanifa.

Aisha ta bayyana hakane sakamakon wani bidiyo na Shahararren Malamin addinin Islama din nan na jihar Kano, Sheikh Dr Abdallah Gadon Kaya, wanda ya bukaci a yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe