29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Zan cigaba da fafutukar ƙwatar ‘yancin sanya Hijabi a ƙasar Indiya -Muskan Khan ɗaliba mai kishin Musulunci

LabaraiZan cigaba da fafutukar ƙwatar 'yancin sanya Hijabi a ƙasar Indiya -Muskan Khan ɗaliba mai kishin Musulunci

Wata ɗaliba musulma mai suna Muskan Khan, wacce ta fuskanci tsangwama a wurin masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu akan hanyarta ta zuwa makaranta sanye da hijabi, a jihar Karnataka, ƙasar Indiya, ta bayyana cewa su na rera mata waka “Jai Shri Ram” saboda ta sanya hijab.

Nima sai na ce Allahu Akbar. Zan cigaba da fafutukar neman ‘yancin sanya hijab.

Hijab
Muskan Khan ɗaliba mai fafutukar ƙwatar ‘yancin sanya hijab. Hoto daga TheIslamicInformation

An samu hatsaniya sosai a jihar Karnataka ranar Talata bayan an wallafa a shafin Twitter wani bidiyon wata ɗaliba musulma sanye da hijab ta sha tsangwama a wurin masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu.

Kamar yadda aka gani a cikin bidiyon, wasu gungun maza sanye da adiko sun kewaye Muskan Khan. Sai dai ba ta karaya ba inda ta cigaba da bayyana matsayar ta. Ta faɗa cewa mafiya yawan yaran ba ‘yan makarantar ba ne.

Musulmai sun ƙi amincewa da dokar hana sanya hijab

Ɗalibai Musulmai sun ƙi amincewa da dokar hana sanya hijab a wannan makarantar ta jihar Karnataka. Su na ganin dokar a matsayin wani hari akan damar gudanar da addinin su kamar yadda kundin tsarin ƙasar ya ba su dama.

Duk lokacin da masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu, su kayi yunƙurin hana ɗalibai musulmai shiga cikin makarantun, ana samun barkewar rigingimu.

Bayan aukuwar lamarin ranar Talata, Muskan Khan gidan talabijin ɗin NDTV cewa:

Aikin aijin da aka bamu naje miƙawa shiyasa na shiga makaranta, amma sun hanani shiga saboda ina sanye da hijab. Sun fara waƙoƙi suna cewa “Joy Shri Ram.” Nima sai na faɗi Allahu Akbar.

Ta bayyana cewa za ta cigaba fafutukar ƙwatar ‘yancin ta na sanya hijab.

Musulmai na cikin halin fargaba a jihar

A ranar Talata gwamnatin jihar Karnataka ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar masu tsaurin addinin Hindu ta Bharatiya Janata Party (BJP), ta sanar da kulle makarantu na tsawon kwana uku.

Wannan lamarin da ke faruwa a jihar Karnataka, ya sanya halin ɗar-ɗar a wajen musulmai waɗanda sune ‘yan tsiraru a jihar. Suna tsoron samun karuwar tsangwama daga gwamnatin ƙasar ƙarƙashin jagorancin firaminista Narendra Modi.

A watan da ya gabata, an faɗa wa ɗaliban da ke zuwa makarantun gwamnati ka da su sake sanya hijab. Tun wannan lokacin masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu su ke ƙoƙarin hana ɗaliban da su ka sanya hijab shiga cikin makarantun jihar.

Musulmai na ta Allah wadai da wannan matakin

Kamar yadda rahotannin cikin gida su ka nuna, makarantu da dama a garin Udupi sun hana ɗalibai musulmai sanye da hijab shiga cikin makarantu inda su ka ce ma’aikatar ilmi ta bada wannan umurnin. Ɗalibai da iyayen su dai sun yi Allah wadai da wannan sabon tsarin.

Ayesha, wata yarinyar ɗaliba a Mahatma Gandhi Memorial College a Udupi, ta bayyana cewa:

Meyasa kwatsam su ke cewa ba zamu sanya hijba ba? Meyasa za su fara hakan yanzu?

Meyasa ba za su iya ƙin yin adawa da kowane addini ba? Ba mu yin adawa da kowa. Muna neman kare yancin mu ne”

Mabiya addinin Hindu na zagin Shahrukh Khan saboda ya yiwa mawakiyar da ta mutu addu’a irin ta Musulmai

Mabiya Addinin Hindu a kasar Indiya sun yi ta zagin shahararren jarumi Shahrukh Khan kan ya yiwa mawakiyar da ta mutu addu’a irin ta Musulmai…

Anyi jana’izar mawaƙiyar Bollywood, Lata Mangeshkar, a dandalin Shivaji, birnin Mumbai na ƙasar India a ranar 6 ga watan Fabrairun 2022. Jana’izar ta samu halartar manyan jarumai daga masana’antar ta Bollywood ciki kuwa harda babban jarumi Shahrukh Khan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe