34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Matashi ya rotse kan mahaifinshi da tabarya ya mutu har lahira a jihar Yobe

LabaraiMatashi ya rotse kan mahaifinshi da tabarya ya mutu har lahira a jihar Yobe

A jiya Laraba 9 ga watan Fabrairu 2022, Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ta ruwaito cewa wani matashi dan shekara 20, mai suna Mai Goni, ya kashe mahaifinshi, Goni Kawu da tabarya a Masaba, cikin karamar hukumar Bursari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, shine ya sanarwa da Kamfanin Dillancin Laabarai na Najeriya (NAN), cewar lamarin ya faru ranar Talata da misalin karfe 7:30pm na dare.

Ya ce Kawu mai shekaru 65 ya samu buguwa a kanshi sakamakon duka da dan yayi masa da tabarya, inda daga baya kuma aka bayar da rahoton mutuwar shi a asibiti.

ASP Abdulkarim ya bayyaana cewa matashin ya gudu bayan aikata wannan danyen aiki, inda ya kara da cewa tuni jami’an su sun bazama neman shi.

Kwaya yake sha yana neman halaka ni, shi yasa na kashe shi – Cewar mahaifiyar da ta kashe dan cikinta

Wata mata mahaifiyar yara uku mai shekaru 49, ta amsa laifin ƙitsa yadda za halaka ɗan ta inda ta bayyana cewa shan ƙwayoyi ya ke yi kuma yana takurawa rayuwar ta.

Ziningi Jane Nzama, wacce za ta yi shekaru 20 masu zuwa cikin gidan kaso, ta faɗawa babbar kotun Pietermaritzburg, dake kasar Afrika ta Kudu, cewa ɗan na ta Asanda Kwanda mai shekaru 20 a duniya, ya zama alaƙaƙai a gare ta tun bayan mutuwar mahaifin sa a watan Janairun shekarar 2020.

Ta bayyana cewa ɗan ta ya fara shan ƙwayoyi sannan yana ɗaukar motocin gidan ba tare da izni ba.

Nzama, wacce ta cigaba da gudanar da sana’ar taxi ɗin mijinta, ta faɗa cewa yaron nata zai lalata motocin sannan ya jira sai ta biya kuɗin gyara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe