34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Hanifa: Aisha Buhari ta kai ziyara Kano, tace dole a yi adalci

LabaraiHanifa: Aisha Buhari ta kai ziyara Kano, tace dole a yi adalci

Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, a yammacin Larabar da ta gabata ta ziyarci jihar Kano domin jajanta wa gwamnati, iyalai da al’ummar jihar kan rashin Hanifa Abubakar mai shekaru biyar da kuma ta’aziyyar fitaccen malamin nan, marigayi Ahmad Bamba.

A wata zantawa da manema labarai da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, Aisha ta ce da gangan ta kai ziyarar ta sirri ne domin yin ta’aziyyar ga iyalan biyu.

Hanifa: Aisha Buhari ta kai ziyara Kano, tace  dole a yi adalci
Hanifa: Aisha Buhari ta kai ziyara Kano, tace dole a yi adalci

“Na zo ziyarar sirri ne domin yin ta’aziyya ga gwamnan Kano da matarsa; Mai Martaba Sarkin Kano da Al’ummar Jahar Kano bisa rashin Sheikh Ahmad Bamba da kuma Hanifa Abubakar wadda bata da laifi, muna fata da addu’ar Allah ya sa a yi mata adalci.

“A matsayina na uwa, ina da ’ya’ya da jikoki a makarantar firamare. Sun amince da malamansu sosai, mu ma haka. Don haka, a yanayin yaranmu ba su da tsaro a makarantunsu, hakan na nufin al’umma ta zama wani abu daban. Ina ganin ya kamata a yi hukunci domin a gamsar da dukkan al’ ummar Najeriya.”

A lokacin da yake gode mata bisa ziyarar, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa uwargidan shugaban kasar cewa, tabbas za a yi adalci.

“Hanifa ‘yar mu ce kuma ta ‘yan Najeriya. Mun damu kuma mun ji dadin ziyarar tun daga Abuja. Ko a lokacin da abun ya faru, kun sanarwa manema labarai cewa kuna fatan gwamnati za ta dauki matakan da ya dace don ganin an gurfanar da masu laifin .”

Tsoro ya sa iyayen wanda ya halaka Hanifa tserewa daga matsugunin su

Tsoro ya sanya iyayen Abdulmalik Tanko wanda ya halaka Hanifa Abubakar, tserewa daga matsugunin su.

A wata ziyara da jaridar Daily Trust ta kai unguwannin Tudunwada da Tudun Murtala inda Abdulmalik ya taso da kuma gidan mahaifan sa, maƙwabta sun bayyana cewa ba san inda iyayen na sa su ka tafi ba.

Wata majiya ta kusa da iyayen na sa ta bayyana cewa a dalilin ta’asar da ɗan su ya tafka ta sace Hanifa da kuma halaka ta, akwai yunƙurin kai musu hari. Wannan ya sanya dole iyayen na sa su ka tsere daga matsugunin su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe