23.8 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Miji na bai min saki uku ba inji Maimuna matar Ado Gwanja, matsalar mu ce ta cikin gida inji Ado Gwanja

LabaraiKannywoodMiji na bai min saki uku ba inji Maimuna matar Ado Gwanja, matsalar mu ce ta cikin gida inji Ado Gwanja

A jiya mun kawo muku labarin wata jita-jita da muka ji tana yawo batun saki uku da aka bayyana Ado Gwanja ya yiwa matarsa Maimuna, wanda labarin yayi matukar taba zukatan masoyan su.

A cikin rahoton muka kawo muku wasu abubuwa da masoyan jaruman suka fahimta wadanda ke tabbatar da cewa alakar dake tsakaninsu tayi tsami.

A kokarin da Tashar YouTube ta Tsakar Gida tayi na bibiyar wannan lamari don sanin hakikanin halin da masoyan suke ciki, sunyi gam da katar, domin kuwa ita da kanta Maimuna matar Ado Gwanja ta tuntube su a shafinsu na Instagram, inda ta yi musu karin haske game da abin dake faruwa tsakaninta da mijin nata.

Komai da ya faru kaddara ce daga Allah

Maimuna ta tabbatar da cewa komai da yake faruwa mukaddari ne daga Allah, inda take cewa:

“Idan ma misali sakin aka yi ai kaddara ce tana kan kowa.”

Kana ta bayyana cewa ita da mijinta har yanzu suna son junan su, wani tsautsayi ne kawai ya gifta har ta kai ga ya sallame ta tafi gidan su, inda ta bayyana cewa ba za ta iya bayyana ko menene makasudin sabanin na su ba, domin tana son mijinta, ba ta son abinda zai saka wasu su zage shi ko a zage ta, saboda kowa da yadda zai kalli lamarin.

A cikin hirar dai Maimuna tana yawan jaddada yadda take son mijinta da kuma tsoron abinda zai taba mutuncinsa ko nata, amma ta tabbatar da cewa a yanzu haka bata gidan shi, kuma abinda ya wuce ba ta son yana dawowa.

Ado Gwanja da matarshi Maimuna
Ado Gwanja da matarshi Maimuna – Hoto: Facebook – Maryam Yahya Photos

Tambaya kan anyi sakin ko ba ayi ba?

Da aka yi mata tambaya akan shin da gaske ne anyi sakin, Maimuna ta tabbatar da cewa koda ma ace yayi sakin ba saki uku yayi mata ba, kuma ita bata ga takardar sakin da idon ta ba.

Da aka sake tambayar ta kan zancen tana da labarin sakin, ta bada amsa da cewa tabbas ba saki uku yayi mata ba, yanzu ma haka baya gari ne, amma tana sa ran da zarar ya dawo zai mayar da ita dakin ta domin suna son junan su ita da shi, tsautsayi ne kawai ya gifta da bai kai ya kawo ba.

Mun samu sabani a baya yafi a kirga

Ta kara da cewa sun samu sabani da dama a baya, wadanda sun fi wannan ma, amma hakan bata taba faruwa ba sai a wannan karon. Maimuna ta bayyana cewa lamarin ya faru wasu makonni da suka gabata.

An tuntubi Ado Gwanja a waya

A nashi bangaren Mawaki Ado Gwanja da aka tuntube shi a waya, ya bayar da amsa a takaice, inda ya bayyana cewa karya ne shi bai saki matarsa ba.

Da aka tambaye shi ko akwai wani sabani da ya haddasa wancan jita-jitar, ya bayyana cewa wannan matsalar sa ce ta cikin gida.

Ana yada kishin-kishin mawaki Ado Gwanja ya saki matar shi Maimuna

Wani labari da muke samu marar dadin ji, akwai kishin-kishin din cewa mawaki Ado Gwanja ya saki matar shi Maimuna, inda a wani bincike da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta gudanar ta gano cewa mawakin ya sauwakewa matar tashi, kuma sakin ba daya ba har saki uku.

Tashar Tsakar Gida sun tambayi dalilin sabanin da ya haddasa sakin da tsawon lokacin da aka yi da yin sakin ba su samu wani gamsashshen bayani ba, amma dai sun tabbatar da rabuwar auren masoyan, wanda zai bakanta ran dubunnan masoyan su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe