34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Igbo da Musulmai masu tsatstsauran ra’ayi ba su da bambanci a wurina – Laila St. Matthew

LabaraiIgbo da Musulmai masu tsatstsauran ra’ayi ba su da bambanci a wurina - Laila St. Matthew

Wani faston cocin Katolika, Rabaran Fr. James Anelu na cocin Parish Priest of Holy Trinity ya haramta amfani da wakokin Ibo a cocinsa, wanda hakan ya janyo masa caccaka ta ko ina daga kabilu daban-daban a kafafen sada zumunta.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, bayan ya haramta hakan, a wani taron coci da suka yi, ya dakatar da wakar bauta da aka yi da harshen Ibo inda ya ce ba zai bar ‘yan kabilar Ibo su dinga mamaye maso coci ba.

Duk da dai an dakatar da shi, amma lamarin ya janyo surutai daga cocinan Katolika ta ko ina, inda suka dinga sukar sa akan kabilanci.

rev 1
Yaren Ibo ba su da bambanci da musulmai masu tsatstsauran ra’ayi da ke kwace garuruwan jama’a, Laila St. Matthew

Sai dai wata ‘yar jaridar Najeriya, Moji Danisa ta mara masa baya inda ta zargi ‘yan kabilar Ibo da yunkurin mamaye duk inda suka je.

Wata mai rajin kare hakkin mata, Laila St. Matthew-Daniel ta nuna goyon bayan ta dari bisa dari ga faston.

Laila ta zargi Ibo da son kwace duk inda suka je, inda a ra’ayin ta tace ba su da bambanci da Musulmai masu tsatstsauran ra’ayi.

Kamar yadda ta furta:

“Akwai Ibo a ‘yan uwa na don haka ba saboda bana son su bane zan yi wannan furucin. Ina son wakokin su amma ba sa min ma’ana saboda bana gane yaren. Maganar gaskiya suna son su mamaye duk inda suka je, a cikin jinin su hakan yake.

“Ba zan iya tuna baturen mulkin mallakan da ya ce Ibo suna da taurin kai da kuma kin yarda a mulke su ba, yayin bayani dangane da yaruka. Ibo ba sa da bambanci da Musulmai masu tsatstsauran ra’ayi masu son mallake duk inda suka je.”

Ta kara da cewa ba za ta duba tsokacin jama’a ba don ta san zata sha caccaka ko ta ina, amma hakan shi ne gaskiya saboda ta ga hakan a kan ‘yan uwanta na jini.

An kai wani farmaki a maƙabartar Musulmai a kasar Jamus

An kai hari wata maƙabartar musulmai a birnin Iserloun, na ƙasar Jamus, inda aka lalata ƙaburbura da dama.

Yayin harin, wanda ya auku a lokacin bikin sabuwar shekara, wasu mutane biyar da ba a san ko su waye ba, sun farfasa ƙaburburan musulmai inda su ka lahanta maƙabartar da ke birnin Iserloun.

A ranar Asabar ‘yan sanda da masu bincike sun sanar da cewa, kusan ƙaburbura talatin aka rushe sannan aka lalata fulawoyin kwalliyar rukunin musulmai na babbar maƙabartar Iserloun.
Lamarin ya auku ne tsakanin yammacin ranar Juma’a zuwa safiyar ranar sabuwar shekara.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe