34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Naira 620 ne albashina na farko lokacin ina Malamin jami’a, cewar mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo

LabaraiNaira 620 ne albashina na farko lokacin ina Malamin jami’a, cewar mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda komai ya sauya a Najeriya inda ya tuna da shekarar 1981.

Ya ce a shekarar ne ya fara koyarwa a jami’ar Legas (UNILAG) inda ya ke amsar albashi N620 kamar yadda Leadership News ta ruwaito.

Ya yi wannan bayanin ne a wani taro na 53 wanda kungiyar malaman fannin shari’a na Najeriya ta shirya a jiya cikin Jihar Kano.

yemi
N620 ne Albashina na farko lokacin ina malamin jami’a, Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo

Kamar yadda yace:

“Bari in fara da godiya ga jiga-jigan kungiyar mu bisa gayyata ta da suka yi don halartar taro na 53 na kungiyar malaman fannin shari’a.

“Taron kungiyar malamai na fannin shari’ar abu ne wanda na saba da shi. Na fara koyarwa a jami’ar Legas a shekarar 1981 a matsayin mataimakin malamin jami’a, kuma albashi na a lokacin N620.”

Osinbajo yace wurin Malaman shari’a na da matukar muhimmanci.

Mune muke tunani da kawo gyara domin a yi adalci

Ya kara da cewa:

“A matsayin mu na malaman fannin shari’a, mu na da ikon samar da salo da ginshikin shari’a saboda mu ke tunani da kuma kawo gyara a fannin adalci da shari’a. Taro irin wannan ya dade yana bayar da dama ga jama’a don su yi tambayoyi dangane abinda ya shige musu akan shari’a da abubuwan da ke kawo hadin kai da zaman lafiyar al’umma.”

Mataimakin shugaban kasar ya ce taken taron wannan shekarar nan: “Shari’a, demokradiyya da kuma yadda ake aiwatar da zabe”, ya dace musamman ganin yadda kasar nan take shirin aiwatar da babban zabe a shekara mai zuwa.

A cewar Osinbajo, demokradiyya ta dade tana fuskanta kalubale a nahiyar Afirka, inda ya bayyana yadda sojoji suka yi juyin mulki a kasashe 12, wanda aka fara a shekarar 2017.

2023: Fastocin Osinbajo da Ganduje na takarar shugaban kasa dake yawo a Kano sun jawo kace-nace

Fastocin kamfen na mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mataimaki sun fara karade jihar Kano gabannin zaben 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an gano fastocin a wurare daban-daban a fadin jihar, ciki kuwa hadda hanyar zuwa filin jirgin sama, da kuma Ahmadu Bello Way kusa da gidan Shekarau.

Haka kuma an gano fastocin a Murtala Muhammad Way, shatale-talen Kano Club, shatale-talen Independence Way da dai sauran wurare daban-daban.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe