27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

‘Yar gidan Atiku Abubakar ta gwangaje jarumi Zubby da dambasheshen fili a birnin Abuja ranar Birthday din sa

Labarai'Yar gidan Atiku Abubakar ta gwangaje jarumi Zubby da dambasheshen fili a birnin Abuja ranar Birthday din sa

Nana Atiku, diyar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar, ta yi wa jarumin fina-finan Nollywood, Zubby Michael kyautar fili a matsayin kyautar zagayoyar ranar haihuwarsa inda ya cika shekaru 37 a duniya.

Ya wallafa a shafinsa

Da yake bayyanawa a shafinsa na Instagram, Zubby ya daura wani hoton su tare da Nana Atiku, inda ya wallafa cewa an ba shi kyautar fili, kyautar da ya yiwa lakabi da “Kyautar cake da yafi kowace kyauta dana taba samu a rayuwata.”

Jinjinar yabo

Jarumin ya yaba wa Nana, wacce ta kasance ’yar kasuwa ce, yana mai cewa:

“Kyautar cake da tafi kowace kyauta da na taɓa samu. NANA ATIKU ta min kyautar fili a Abuja a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwa ta @nanaatiku_kadi. Na gode kwarai da wannan kyauta na gode kuma ALLAH Ya saka da alheri.”

Diyar Atiku Abubakar ta yiwa Zubby Micheal kyauta
Diyar Atiku Abubakar ta yiwa Zubby Micheal kyauta

Haka ita ma a na ta bangaren, Nana Atiku, a karkashin sharhin sakon da aka sanya sunanta, ta rubuta cewa:

“Ana tare.”

Nana ta kuma wallafa wasu hotunan ta tare da Zubby a shafinta na Instagram yayin da take ta ya shi murna.

Ta rubuta:

“Ina tayaka murnan ranar haihuwan ka ɗan wasan da na fi so. Mutum mai zuciyar zinari. Ina maka fatan kasancewa cikin farin ciki ko yaushe. Allah ya kara maka budi a duk sanda kayi ihsani kai ma. Kullum ina alfahari da kai. Happy birthday dan uwana. Allah ya albarkaci shekarun ka.”

A cikin fim din Zubby Micheal na koyi yadda ake garkuwa da mutane – Cewar matashi da ya sace dan shekara 6

Wani matashin saurayi da rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama da laifin sace wani yaro dan shekara 6, ya bayyana cewa ya koyi yadda ake garkuwa da mutane a wajen jarumin Nollywood Zubby Michael, wanda yake yawan fitowa a matsayin mai garkuwa da mutane a cikin fim.

Saurayin da aka bayyana sunan shi da Ayobamidele Kudus Ayodele ya sace yaron a makarantar su dake Ojo, cikin yankin Alaba dake jihar Lagos, a ranar 16 ga watan Nuwambar shekarar 2021.

Bayan sace yaron Kudus ya ajiye yaron na tsawon kwana hudu a hannun shi har zuwa lokacin da aka biya shi sama da dubu dari biyar a matsayin kudin fansa kafin ya saki yaron.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe