29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Wani yaro da aka dorawa talla ya zama abin sha’awa bayan ya ajiye kayan tallar ya dukufa wajen neman ilimi

LabaraiWani yaro da aka dorawa talla ya zama abin sha'awa bayan ya ajiye kayan tallar ya dukufa wajen neman ilimi
  • Wani mutum ya yada bidiyon wani yaro yana tsugunne a gefen titi yana aikin makaranta tare da sai da kayan tallarsa
  • Ogwu ya bayyana cewa ya dade yana ganin wannan yaro yanayin aikin makarantarsa gefen titi
  • Don haka mutumin yayi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su agaza wa yaron ya samu ilimi mai kyau

Wani dan Najeriya mai suna Hon Ogwu Austine ya ba wa gidan Jaridar Legit.ng faifan bidiyon wani yaro dan talla. Mutumin yana fatan yaron zai samu duk wani taimakon da ya dace

A cikin faifan bidiyon, an nuno yaron ya ajiye tiren kayan tallar da aka dora masa a gaban wani gini da ba kowa domin yin aikin da aka bashi a makarantan.

Ko yaushe mutumin yana ganin yaron yana aikin makarantansa

Da mutumin ya tambaye shi abin da yake yi, cikin muryar tsoro rike da littafinsa a hannunsa ya ce yana aikin da aka bashi a makaranta ne.

Ogwu ya bayyana cewa ba wannan bane karo na farko da ya fara ganin yaron a kusa da makarantar shi ta Michael Okpara University of Agriculture Umudike.

Yaron yana da sha’awar koyon ilimi

Mutumin ya ce duk da irin nauyin tallar da aka daura ma masa, hakan bai hana shi kwadayin neman ilimi ba.

Ya ce:

“Wani lokaci a makon da ya gabata, na hadu da shi kamar yanda muka saba haduwa yana rike da littafinsa na rubutu yayin da yake saida wa Mahaifiyarsa Agada, da hakan har yana iya yin aikin da aka bashi a makaranta, kawai sai naji abun ya burgeni, na fahimci irin matsayin da ya bama ilmi saboda yawan ganinsa da nake yi yana aiki.

Yana da tsananin sha’awar neman ilim. Hakan yasa nadan yi masa ‘yan tambayoyi kadan akan sa da kuma dalilinsa na yawan yin karatu akan titi. Sai na gano cewa kwazonsa na neman ilimi ba zai misaltu ba duk da cewa iyayensa basu da karfi”.

Yadda takaici ya sanya wani mutumi fashewa da kuka bayan ya ga wasu yara kanana na talla akan titi

A cikin Wani faifan bidiyo da @ssussjamofficial ya yada shi a kafar sada zumunta ya haska inda aka ga wani mutum ya na nuna tausayawar sa ga wasu yara, yayin da ya gansu suna yawon talla a bakin hanya.

An gano mutumin ya sauko daga cikin motar sa ya rungumi yaran cikin yanayi na tausaya musu kan halin da suke ciki.

Sakamakon rungume yaran da yayi ya sanya suka dinga kokwanton ko yaran sun tunawa da mutumin lokacin yarintar shi ne.

Yanayin na ban tausayi ya sanya mutane da dama suka yi ta magana, bayan an gan shi yana bin yaran daya bayan daya yana rungume su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe