36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

‘Yan bindiga sun sace wata mata tare da ɗiyarta a jihar Bauchi

Labarai'Yan bindiga sun sace wata mata tare da ɗiyarta a jihar Bauchi

Waɗansu ‘yan bindiga sun sace wata mata, Khadija Audu-Ardo, mai shekaru 40 a ƙauyen Tsamiya na yankin Boi, a ƙaramar hukar Bogoro, jihar Bauchi. Jaridar PUNCH ta ruwaito.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’an tsaron haɗin guiwa da ke a yankin Boi, ƙaramar hukumar Bogoro, su ka ba ‘yan jarida ranar Talata a Bauchi.

'Yan bindiga sun ɗauke wata mata a jihar Bauchi
Taswirar jihar Bauchi. Hoto daga Punch

A cewar sanarwar, matar an ɗauke ta ne tare da ɗiyar ta zuwa wani wuri da ba’asan ko ina ba ne a daren ranar Litinin.

Da misalin ƙarfe 12 na dare, mazauna ƙauyen sun kawo mana rahoton sace Khadija Audu Ardo wanda wasu mutane ɗauke da manyan bindigu su kayi.

Mun tura jami’an mu zuwa ƙauyen da gaggawa. Yanzu haka da na ke magana da ku, muna iyakar ƙoƙarin mu wajen ceto rayuwar matar da kuma ta ɗiyar ta.

Wani mazaunin ƙauyen na Tsamiya, ya shaida cewa:

Mu na cikin tsoro tun bayan aukuwar wannan lamarin ranar Litinin. Yan bindigan sun shigo da daddare sannan su ka ɗauke Khadija da ɗiyarta .

Mijin matar ba ya gida lokacin da ‘yan bindigar su ka zo


Mijin Khadija, Audu Ardo, ya bayyana cewa yaje duba shanayen sa a ƙauyen da ke maƙwabtaka da su inda ya kwana a can.

Bani da masaniya cewa wani abu zai auku. Na bar gida lokacin da su ka zo. Ina roƙon waɗannan masu garkuwa da mutanen da su taimaka su sakar min matata da ɗiyata domin ba su yi musu laifin komai ba.”

Magajin garin ya nuna damuwar sa

Magajin garin Boi, Bala Likita, ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro matuƙa.

Na kaɗu matuka cewa a karon farko masu garkuwa da mutane sun samu damar shigowa yanki na. Muna rokon Allah ya kare mu” a cewar sa

Saboda nama da sauran kayan dadin da ‘yan bindiga suke ba shi, dalibin Bethel Baptist ya ki yarda ya komawa gida

Dalibi daya na makarantar Bethel wanda ya rage a hannun ‘yan bindiga ya murje idanun sa, ya ce yana jin dadin zama da ‘yan bindiga saboda kayan tagomashin da yake samu a wurin su, Vanguard ta ruwaito.

Yayin da ‘yan kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, suka tattara kudin fansar da ‘yan ta’addan suka bukata, ‘yan bindigan sun damke wanda ya je kai sakon.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe