Wani labari da muke samu marar dadin ji, akwai kishin-kishin din cewa mawaki Ado Gwanja ya saki matar shi Maimuna, inda a wani bincike da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta gudanar ta gano cewa mawakin ya sauwakewa matar tashi, kuma sakin ba daya ba har saki uku.
Tashar Tsakar Gida sun tambayi dalilin sabanin da ya haddasa sakin da tsawon lokacin da aka yi da yin sakin ba su samu wani gamsashshen bayani ba, amma dai sun tabbatar da rabuwar auren masoyan, wanda zai bakanta ran dubunnan masoyan su.
Maimuna ta cire abubuwan da suka shafi Ado Gwanja a shafinta
Haka kuma a wani bincike da Tashar Tsakar Gida ta sake gudanarwa a shafin Maimuna, sun gano cewa ta cire duk wani abu da ya shafi Ado Gwanja a shafinta, hatta sunan Ms Ado Gwanja da ta sa ta cire ta sa sunan “Fashion Beauty”, haka shafin da take kasuwancin ta mai suna “Munat Gwanja Collection” shi ma ta canja shi zuwa “Munat Dan’auta Collection”.

Baya ga wannan, sanin kowane jarumin kan shirya kasaitaccen bikin “Birthday” ga matar tashi da ‘yar sa duk shekara, amma wannan shekarar Maimuna ita kadai tayi ‘yan hotunanta ta wallafa a shafin ta, kuma Ado Gwanja bai taya ta murna a shafin shi ko sashen tsokacin ta ba.
Bugu da kari a watan da ya gabata, mahaifiyar Maimuna ta rasu shi ma ta wallafa a shafin ta jaruman Kannywood na ta yi mata ta’aziyya, amma Ado Gwanja bai ce komai ba, haka kuma bai wallafa a shafinsa ba.
Ado Gwanja ya bayyana BBC Hausa ba zai yi mata kishiya ba
Haka kuma kowa dai yasan irin soyayyar da shakuwar da masoyan ke bayyanawa juna a shafukan sada zumunta, domin har hira BBC Hausa ta yi da Ado Gwanja, inda ya tabbatar da cewa ba zai yiwa matar sa kishiya ba.
Baya ga haka, kowa ya san yadda jarumin yake yawan wallafa hotunan matarshi tare da rubuta kalamai na soyayya da yake mata.
Haka ita ma an gano hotunan ta da bidiyo a wuraren shakatawa ba tare da siffa ta matar aure ba
Ado Gwanja – Sakon mu ya fi na Malamai isa ga al’umma
Wani shafi mai suna Punch Hausa a dandalin Facebook ya kawo labarin wata hira da suka yi da mawaki kuma jarumi Ado, a cikin hirar jarumin ya bayyana cewa sakon su masu harkar nishadi yafi saurin isa ga al’umma fiye dana Malamai, inda ya bada hujjojin sa.
Sai dai kuma wannan lamari ya zama abin muhawara a shafin, inda wasu ke ganin batun na Ado Gwanja akwai kamshin gaskiya a ciki, wasu kuma suke ganin cewa soki burutsu ne, inda suke ganin bai kamata ya kwatanta Mawaka da Malamai ba
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Facebook Page
Twitter Page
Telegram Channel
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com
Allah yakyuata