24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Mabiya addinin Hindu na zagin Shahrukh Khan saboda ya yiwa mawakiyar da ta mutu addu’a irin ta Musulmai

LabaraiMabiya addinin Hindu na zagin Shahrukh Khan saboda ya yiwa mawakiyar da ta mutu addu'a irin ta Musulmai

Mabiya Addinin Hindu a kasar Indiya sun yi ta zagin shahararren jarumi Shahrukh Khan kan ya yiwa mawakiyar da ta mutu addu’a irin ta Musulmai…

Anyi jana’izar mawaƙiyar Bollywood, Lata Mangeshkar, a dandalin Shivaji, birnin Mumbai na ƙasar India a ranar 6 ga watan Fabrairun 2022. Jana’izar ta samu halartar manyan jarumai daga masana’antar ta Bollywood ciki kuwa harda babban jarumi Shahrukh Khan.

A lokacin da aka ba Shahrukh Khan damar yin addu’a, jarumin ya matsa kusa da gawar inda yayi addu’a sannan ya tofa a duk ilahirin jikinta, wanda hakan dabi’a ce a cikin addinin Musulunci.

Jarumi Shahrukh Khan
Jarumi Shahrukh Khan. Hoto daga Instagram @iamsrk

Shahrukh Khan yasha suka wajen ‘yan addinin Hindu

Sai dai masu tsaurin ra’ayin addinin Hindu, Hindutva, da kuma magoya bayan jam’iyyar BJP, sun mayar da abin zuwa ƙin jinin addinin Musulunci. Sun yi iƙirarin cewa jarumin ya tofa mata yawu ne wanda hakan cin mutunci ne ga Lata Mangeshkar.

Musulmai da yawa a kafafen sada zumunta sun kare jarumin inda su ka faɗa cewa yin addu’a da tofawa ba sabon abu ba ne. Wannan ƙin jinin addinin musuluncin da ake nunawa a ƙasar ta India ya kai ga har babban jarumi a masana’antar ta Bollywood na fuskantar ƙalubale wajen yin addinin sa.

Shafin Arun Yadav ne dai ya fara wallafa labarin ƙaryar cewa Shahrukh Khan ya tofa wa gawar yawu.

Prashant P Umrao, mai magana da yawun jam’iyyar BJP a Uttar Pradesh, ya sa ke wallafa maganar Yadav inda ya ƙara da cewa “jarumin yana tofa yawu”. Sai dai a baya an sha ganin Umrao yana yaɗa labaran ƙarya.

Shahrukh Khan ya samu goyon baya

An samu mutane da dama waɗanda su ka nuna goyon bayan su kan Shahrukh Khan.

Nida Kimani ta rubuta:

Shahrukh Khan ya karanta addu’a wurin jana’izar Lata Mangeshkar amma ‘yan jam’iyyar BJP da ‘yan Hindutva na masa sharrin ya tofa wa gawar yawu ya nuna haƙiƙanin abinda ƙasar India ta zama

Sanjoy K Roy ya rubuta:

Duk da ana cikin jin zafi da jimamin mutuwa, sojojin cin zarafi da masu nuna tsana sun yi aikin su inda su ka hari Shahrukh Khan, duk da yayi addu’oi ga Lata Mangeshkar wacce ta zama wakiliyar ainihin waƙa, wacce ba ta da addini ko yare.

Ashoke Pandit ya rubuta cewa:

Waɗanda ke sukar Shahrukh Khan ta hanyar yi masa ƙagen tofawa gawar Lata Mangeshkar yawu, sun yi abin kunya. Yayi addu’a sannan ya shafa a gawar domin samun kariya da albarka ga wannan tafiya ta ta. Wannan ƙazantar ba ta da wuri a ƙasa irin ta mu

An kama dan kasar Indiya da yake sayar da mata Musulmai a kafar sadarwa

An yi ram da wani mutum dan kasar Indiya wanda ya yada hoton wata Musulma domin siyarwa akan wata manhaja mai suna Bulli Bai.

‘Yan sandan kasar Indiyan sun sake cafke wata mata ‘yar Garin Uttarakhand wacce ake tuhumarta akan aikata wannan aika aikar.

Wanda ake Tuhuma Mai Suna Vishal Jha, an cafke shi ne a Bengaluru kafin daga baya, aka mai da shi Mumbai a ranar 3 ga Janairu, 2022, yanzu haka yana tsare ana bincikarsa. Za a ci gaba da tsare sa a hannun ‘yan sanda har zuwa ranar 10 ga Janairu, 2022.

Har ila yau, matar da aka cafken tana nan a tsare ana gudanar da bincike a kanta. An kama ta ne bisa dalilin tarayyar ta da Vishal Jha.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe