24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Sarkar gwal ta Naira miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikarta

LabaraiAl'adaSarkar gwal ta Naira miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikarta

A makon da ya gabata ne dai aka yi bikin sunan jikar Jaruma Hafsat Idris, inda aka mayarwa da jikar sunan ta, wato Hafsat. Sai dai kuma shagalin bikin sunan ya dauki hankula matuka, ganin yadda cewa wani bikin auren ma bai kai taron sunan yawan jama’a ba, musamman jaruman Kannywood mata.

Uwar mai jegon tayi fita ta kece raini da tsadajjen leshi mai dan karen kyau da sarkar gwal da aka yi kiyasin cewa kudin ta ya kai kimanin naira miliyan goma sha daya (N11m).

Jaruma Hafsat Idris
Jaruma Hafsat Idris (Barauniya) – Hoto: Instagram – official_hafsat_idris

Shafin labaran Kannywood dake dandalin Twitter ne ya tabbatar da hakan, inda suka wallffa hoton jarumar tare da rubuta:

“Sarkar gwal din da jaruma HAFSA IDRIS tasaka a ranar sunan jikar ta (Hafsa Jnr) ance kudin ta yakai Naira Milyan Goma Sha Daya!

“Allah ya kara arziki, Allah kuma ya raya mana Hafsa karama… Amin!

Jarumai mata da dama sun halarci wannan gagarumin shagalin suna irin su Mansurah Isah, Sameera Ahmad, Aina’u Ade, Sadiya Gyale, da dai sauran su.

Ga kadan daga cikin bidiyon wajen bikin:

https://www.instagram.com/reel/CZh26yQpTZ-/?utm_source=ig_web_copy_link

Kamfanin UK Entertainment ya maka Hafsat Idris Barauniya a kotu

Babbar kotu mai lamba 18 da ke zama a garin Ungoggo ta na ci gaba da shari’ar fitacciyar jarumar fina-finai, Hafsat Idris Barauniya da kamfanin UK Entertainment.

Kamfanin na zargin jarumar da amsar musu kudin aiki N1,300,000 ba tare da karasa mu su aiki ba.

Mai shari’a, Zuwaira Yusuf ce ta ke gudanar da shari’ar. UK Entertainment sun bukaci ta biya su diyyar bata musu lokaci da ta yi.

Dama kamfanin ya bayyana yadda su ka mallaka wa jaruma Hafsat Idris kudaden sannan su ka bukaci ta yi musu wani aiki na TV Show, amma shiru suke ji tamkar malam ya ci shirwa.

Kamfanin ya zargi jaruma Hafsat Idris wacce aka fi sani da barauniya da kin yin aikin duk da amshe kudaden da ta yi ba tare da maida mu su ba.

Duk da dai jarumar ba ta halarci kotun ba, Hafsat Idris ta tura lauyanta don ya wakilce ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe