23 C
Abuja
Monday, September 26, 2022

Dalilin da ya sanya na gina makarantar tsangaya ga Almajirai a Arewa – Goodluck Jonathan

LabaraiDalilin da ya sanya na gina makarantar tsangaya ga Almajirai a Arewa - Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana cewa ya rungumi tsarin ilimin makarantun Almajirai ne a lokacin mulkinsa, domin ya shigar da tsarin karatun ilimin Boko cikin tsarin karatun allo, ta yadda zai taimaki Almajiran wajen samun aikin yi, da kuma fatattakar halin rashin tsaro.

Jonathan din ya fadi hakan a ranar Litinin, yayin gudanar da wani jawabi da ya gabatar a wurin taron koli, na ilimin matan jihar Bayelsa, wanda aka yiwa taken ‘Kyautata bayarwa, aiwatarwa da kuma dorarren sakamako a fannin Ilimi’, a garin Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa. 

Maganar tsohon shugaban kasa

Ya ce:

” Lokacin ina matemakin shugaban kasa, na tattauna da wani mataimakina a fanni na musamman, wanda dan Jihar Anambra ne, akan rikicin dake faruwa a Arewa, sai yace ya kamata mu tsara yadda zamu tunkari hakan. 

” Ya tabbata wasu gungun yara sun taso basu da makoma, amma ba zamu kyale hakan ya ci gaba da faruwa ba, domin kada mu fuskanci matsala nan gaba.

 
“Sai muka karade Arewa, muka zanta da malaman da suke koyar da wadannan yara, a karkashin tsangaya, muka gina musu gidaje. Haka kuma, mun tattauna da sarakuna da sauran su. 

Almajirai masu neman ilimi
Almajirai – Hoto: Bulama Cartoon


“Sai muka gano wasu tarin yara wadanda Musulmai ne, su kuma a garin Musulmai idan ka fahimci Al Qur’ani, to ka zarce Farfesa a fannin doka (law).

“Saboda haka, ta karkashin shirin mu na Almajiri, sun fahimci Al Qur’ani kuma baka isa ka raina su ba. 

Wasu daga cikin Musulmai zasu iya haddace Qur’ani


“Kai wasu daga cikin su za suma iya haddace Al Qur’anin baki dayansa, dubu dai girmansa, to kaga kenan mutum ya haddace Qur’ani kai kuma kace dashi bashi da ilimi, to karya kake yi. 

“Su (Almajirai ) sunyi ilimi, amma kuma ana dakile su, ta yadda koda a karamar hukumar su ba za’a iya daukansa aiki koda na dan aike ba (messenger) saboda wai basu da wani burbushi na ilimin boko, tare da wannan ilimin Qur’anin.


“Wannan ne yasa gwamnatin tarayya tace, dole ne mu taimaki jihohin da ake koyawa wadannan yara ilimin addinin Musulunci, ba zamu cire komai daga ciki ba, amma zasu hada da karatun boko saboda idan sun gama wannan matakin, zasu iya ci gaba su karanci likitanci da kere-kere. Wannan shine ya zaburar da mu muka rungumi shirinmu na ilimin tsangaya”. Jonathan ya fada.

Tsohon shugaban yayi kira akan baiwa ilimin fasahar sadarwa mahimmanci

Haka kuma, Jonathan din yayi kira da babbar murya akan a mai da hankali kan kimyya da fasahar sadarwa (ICT)  inda nuna yadda ilimin yake haifar da wadansu bangarori daga cikin sa. 

Da yake kaddamar da bude taron kolin, gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, ya nuna bukatar samun tsayyen harshe, ya kuma yi kira ga taron kolin, da yayi duba ga ababen da aka rasa, sannan ya duba yiwuwar baiwa bangarori masu zaman kansu da su shigo su hada gwiwa da gwamnati wajen cimma burinta akan ilimi.

Goodluck Jonathan: Bindiga kawai ba za ta iya kawo karshen ‘yan bindiga ba

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya shawarci gwamnatin tarayya tayi amfani da fasahar zamani domin duba ga matsalar ‘yan bindiga da kuma sauran ayyuka na ta’addanci da ake fama da su a kasar.

Goodluck Jonathan ya bayar da shawarar ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli, a lokacin bikin murnar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Ossitaa Chidoka, na cika shekaru 50 a duniya, wanda aka gabatar a babban birnin tarayya Abuja, rahoton The Sun.

Tsohon shugaban kasar ya ce bindiga da sauran abubuwan yaki kadai baza su iya hana ‘yan bindiga da barayi daina abinda suke yi ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe