27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Shugabannin jam’iyyar PDP na kula makircin hana Atiku fitowa takarar shugaban kasa a 2023

LabaraiShugabannin jam'iyyar PDP na kula makircin hana Atiku fitowa takarar shugaban kasa a 2023
  • Duk da kamfen din da magoya bayansa ke yi, da alama burin Atiku na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba zai kai ko ina ba
  • Wasu masu fada a ji a jam’iyyar PDP sun ki amincewa da bukatar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku
  • Wasu na ganin shekarun Atiku a matsayin babban dalilin da zai kawo masa cikas

FCT, Abuja – Wani rahoto da jaridar Nigerian Tribune ta fitar ya nuna cewa jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da tsofaffin manyan sojoji sun fito sun bayyana rashin goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Atiku, mai shekaru 75, yana neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jami’iyyar PDP a zaben shekarar 2023 bayan ya tsaya takara a jam’iyyar a shekarar 2019 ya sha kasa.

Yadda wasu daga cikin jiga-jigai kuma tsofafin sojoji masu rike da madafun iko a jam’iyyar tun kafuwar ta a shekarar 1998, su ke kokarin ganin an sauya fuskar wanda zai ja ragamar tutar jam’iyyar.

Atiku Abubakar
Tsohon dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar

Baya ga tsofaffin sojojin akwai wadanda suke da gindin zama a cikin jam’iyyar, tsoffin shugabanni wanda suka kasance suna da tasiri sosai a tafiyar tare da sauran masu rike da madafun iko wanda suka hada kai wajen daukar muhimman shawarwari akan babbar jam’iyyar ta adawa.

A wata tattaunawa da ya yi da masu kula da shige da fice da kuma harkokin jam’iyyar ta PDP a kwanan nan a gidansa da ke Hill Top dake Minna, tsohon shugaban kasa zamanin mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce shi da wasu jiga-jigan sojoji da suka yi ritaya su ne ke rike da bangaren iko na jam’iyyar PDP.

Tsohon shugaban mulkin soja Ibrahim Babangida ya tofa albarkacin bakinsa

Tsohon shugaban mulkin sojan ya kara da cewa bai kamata wanda zai fito takarar shugaban kasa ya haura shekaru 70 ba shi kuma Atiku 75 ya ke.

Haka shi ma tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi kira da cewa duk wanda zai zama shugaba kasa nan gaba ya kamata ya zama yana da zurfin ilimi akan tattalin arziki.

Ka yi hakuri ka kyale irin mu masu jini a jika mu mulki Najeriya – Yahaya Bello ga Tinubu

Janar Abdusalami Abubakar shi ma ya kara nashi inda ya bada shawaran cewa ya kamata ace matashi ne zai fito takarar shugabancin kasar wanda zai iya jan ragamar mulki.

Masu fada aji a yankin kudu suma sun bayyana nasu ra’ayin su

Suma masu fada aji daga yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu sun fito karara sun nuna rashin goyon bayansu ga takarar Atiku, inda suka bukace shi da ya kassance mai duba da kuma adalci.

Wasu ‘yan adawa sun yi ikirarin cewa ya taba tsallakewa ya bar jam’iyyar bayan ta sha kaye a zaben 2019 inda ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) .

Wasu kuma na ganin cewa jam’iyya mai ci za ta iya sake bude wasu batutuwan da za suyi jagora ga yakin neman zaben Atiku tare da wasu hukumomin gwamnati don tunkarar babban zabe mai gabatowa.

Har ila yau, an bada rahoton cewa kasancewar shi dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 ya raba kan gwamnonin PDP, da dattawan kwamitin amintattu, da wasu jiga-jigan jam’iyyar da ke fadin shiyyar kasar, musamman a yankin kudancin kasar.

Haka kuma Sakamakon kasancewar sa dan takara rahotanni sun ce jam’iyyar adawa hakan ya zame mata sanadin hada kan wasu gwamnonin PDP da kuma matasa a cikin jam’iyyar a, yunkurin su na marawa tsohon mataimakin shugaban kasar baya.

Wani dan adawa da Atiku ya bayyana ra’ayinsa shi ma

Wani ginshiki wadanda shima ya kasance dan adawa ga Atiku shi kuma ya bayyana ra’ayinsa cewa ya kamata ace an tsayar da dan matashi mai karancin shekaru a zabe mai zuwa.

Hakazalika, wasu kuma sun yi fatali da duk wata makarkashiyar da za ta kawo cikas ga canjin mulki daga arewa zuwa kudu a shekarar 2023, tunda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance dan yankin arewacin Najeriya ne.

Sai dai kuma magoya bayansa sun yi yunkurin tunkarar wadancan dakarun da ke nuna adawa ga muradin Atiku, suna masu ikirarin cewa shi kadai ne a cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka nuna goyon bayansu akanshi a ba shi tikitin takara a jam’iyyar domin ya zamo wanda zai iya karawa da jam’iyyar APC.

A cewar su yana da duk wani abunda dan takara ke neman wanda zai iya amfani da shi a matsayin makamin da zai yaki jam’iyyar da ke mulki yanzu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe