36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Sadiya Haruna: Za mu je firzin ziyara rike da kullin garin rogo, cewar Teema Makamashi da Fatee Slow

LabaraiKannywoodSadiya Haruna: Za mu je firzin ziyara rike da kullin garin rogo, cewar Teema Makamashi da Fatee Slow

Bayan kotu ta yanke wa Sayyada Sadiya Haruna hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari ba tare da tara ba akan wata rigima da ta shiga tsakanin ta da Jarumi Isah A. Isah, abokan rigimarta sun yi bidiyo suna shewa.

Babban abokin ta na soshiyal midiya, Chizo Germany ya bayyana a wani bidiyo yana yi mata Allah ya kyauta, sannan ya wallafa bidiyon Teema Makamashi, Isah A. Isah da Fati Slow kowa yana tofa albarkacin bakinsa.

isa da sadiya 1
Sadiya Haruna: Za mu je firzin ziyara rike da kullin garin rogo, cewar Teema Makamashi da Fatee Slow

Teema Makamashi ta yi bidiyo ne tana shewa tare da waka inda ta ce karshen alewa kasa. Wakar ta ta tazo kamar haka:

“Idan kasan farkon rikici baka san karshensa ba. Shekara 6 firzin tak! Shekara 6 firzin cak tak! Shekara 6 fizin cak cak!”

Ta ci gaba da cewa ba ta fada sai an tabo ta, ga shi nan dai an yanke wa Sayyada Sadiya Haruna shekara 6 kuma wajibi ne su tanadi garin kwaki, fiyo wota da biredi saboda su kai mata ziyara don ba sa yin gaba.

A bangaren Isah A. Isah kuwa godiya ya yi wa Ubangiji akan nasarar da ya ba shi akan shari’ar inda yace Allah ya wanke shi a idon duniya.

Fati Slow kuwa a wani bidiyo da ta yi ta ce baki shi ke yanka wuya.
Kamar yadda ta yi maganganun cike da farin ciki da annashuwa a fusakar ta inda ta fara da sallama sannan tace su musulmai ne ba sa yin gaba.

Sannan ta ci gaba da cewa:

“Yanzu gamu a hanya mun sayi garin rogo, mun sayi biredi, mun sayi fiyo wota, mun sayi kuli-kuli, mun sayi gyada, mun sayi siga, zamu tafi firzin ziyara.”

Ta ci gaba da cewa dama baki shi ke yanka wuya. Ta ci gaba da cewa har kwana wasu suka yi suna zagin su ga shi yanzu gaskiya ta yi halin ta.

Kotu ta yanke wa Sadiya Haruna hukuncin watanni 6 a gidan yari saboda batanci ga Isah A. Isah

A ranar Litinin wata kotun majistare da ke filin jirgin Mallam Aminu Kano ta yanke wa wata fitacciyar jarumar Kannywood kuma sananniya a Instagram, mai suna Sadiya Haruna hukuncin wata shida a gidan yari akan cin zarafin wani jarumin Kannywood, mai suna Isah Isah da tayi, Daily Nigerian ta ruwaito.

An samu labarin yadda jarumar ta zage Isah a Instagram sannan ta yada a kafafen sadarwa, inda tayi amfani da kalamai marasa dadi, hakan ya tunzura shi ya dauki matakin da ya dace.

Daily Nigerian ta tattaro bayanai akan yadda jarumar a wani bidiyo da ta wallafa a shafin ta na Instagram ta zargi Isah da yin auren mutu’a da ita, yayin da ya sadu da ita ta baya ba da son ranta ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe