27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Daurin Sadiya Haruna nasara ce a gare ni, cewar Jarumi Isah A. Isah

LabaraiKannywoodDaurin Sadiya Haruna nasara ce a gare ni, cewar Jarumi Isah A. Isah

Jarumin fina-finan Kannywood, Isah A. Isah wanda aka daure Sayyada Sadiya Haruna saboda shi ya fito ya nuna farin cikinsa karara dangane da hukuncin da kotu ta yanke.

Idan ba a manta ba, shekaru 2 kenan da watanni 3 bayan Sayyada Sadiya Haruna ta bayyana a wasu bidiyoyi da ta wallafa a kafafen sada zumunta tana maganganu akan Isah.

A lokacin, Sadiya Haruna ta zarge shi da yin auren mutu’a da ita, shafa mata cuta da kuma yin amfani da ita ta bayan ta ba tare da yardar ta ba.

sadiyya haruna 2
Daurin Sadiya Haruna nasara ce a gare ni, cewar Jarumi Isah A. Isah.

Ta kira shi da dan luwadi, mazinaci, shege da sauran maganganu wadanda ko a lokacin ya bayyana a wani bidiyo yana musanta duk kalaman nan inda ya lashi takobin sai ya dauki matakin shari’a akan ta.

A ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairun 2022 ne labarin hukuncin da kotu ta yanke wa jarumar ya bazu jim kadan bayan jarumar ta bayyana a bidiyo tana yin wata wakar yabon ma’aiki.

A daren Talata, shafin Princess Mufeedah na Facebook ya wallafa bidiyon Isah A. Isah yana mika godiyarsa ga masoya, ‘yan uwa da abokan arzikin da suka taya shi addu’a akan lamarin.

Kamar yadda ya ce a farkon bidiyon:

“Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barakatuhu. ‘Yan uwa da abokan arziki, masoyana wanda na sani da wanda ban sani ba, wanda suke taya ni addu’a. Yau ranar Litinin, 7 ga watannan na turawa da muke ciki, February.

“Shari’a ta da wannan yarinyar da ta shiga soshiyal midiya yau shekara 2 da wata 3 da ‘yan kwanaki, ta shiga ta ci min mutunci ta kuma min kazafi, Alhamdulillah yau muna kotu da ita shekara 2 da ‘yan watanni.

“Yau kotu ta yi hukunci, ta wanke ni, ta kama ta da laifi, ta amsa laifinta, Alhamdulillah ala kulli halin, kotu ta daure ta wata 6 ba tara. Ina yiwa Allah godiya, wannan Allah ne ya yi min hukunci. Allah ne ya min sakayya. Dama kullum ina gaya masa, in har an zalince ni, Allah ka bi min hakki na.”

Ya kara da cewa yau Allah ya tabbatar da wanke shi a duniya. Ya yi gidiya ga masoyan sa masu taya shi addu’a dangane da lamarin.

Kotu ta yanke wa Sadiya Haruna hukuncin watanni 6 a gidan yari saboda batanci ga Isah A. Isah

A ranar Litinin wata kotun majistare da ke filin jirgin Mallam Aminu Kano ta yanke wa wata fitacciyar jarumar Kannywood kuma sananniya a Instagram, mai suna Sadiya Haruna hukuncin wata shida a gidan yari akan cin zarafin wani jarumin Kannywood, mai suna Isah Isah da tayi, Daily Nigerian ta ruwaito.

An samu labarin yadda jarumar ta zage Isah a Instagram sannan ta yada a kafafen sadarwa, inda tayi amfani da kalamai marasa dadi, hakan ya tunzura shi ya dauki matakin da ya dace.

Daily Nigerian ta tattaro bayanai akan yadda jarumar a wani bidiyo da ta wallafa a shafin ta na Instagram ta zargi Isah da yin auren mutu’a da ita, yayin da ya sadu da ita ta baya ba da son ranta ba.


Haka zalika, ta kira shi da mazinaci, dan luwadi, shege da sauran munanan maganganu.
An gurfanar da ita ne a gaban kotu a ranar 16 ga watan oktoban 2019, inda ake tuhumarta da bacin suna wanda yaci karo da sashi na 391 na kundin tsarin shari’a.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe