36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ba ni da niyyar fitowa takarar shugaban kasa, mukamin da darikar Tijjaniyya suka bani ya ishe ni – Sunusi Lamido Sunusi

LabaraiBa ni da niyyar fitowa takarar shugaban kasa, mukamin da darikar Tijjaniyya suka bani ya ishe ni - Sunusi Lamido Sunusi
  • Tsohon sarki kano sanusi II ya yi wasu muhimman jawabi ga me da kalubalen da Najeriya ke fuskanta
  • Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN yace ba yi da sha’awar maye gurbin Buhari a shekarar 2023
  • Duk da haka, Sanusi ya aike da muhimmin sako ga masu burin dalewa kujerar shugabancin kasar

Abeokuta, jihar Ogun – Sarkin Kano na 14, Alhaji Muhammadu Sunusi II, ya musanta zargin da ake masa na neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023, yana mai cewa kasancewarsa jagoran darikar Tijjaniyya kawai ma ya isheshi.

Sunusi ya bayyana haka ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake amsa tambayoyi a wajen wani liyafar bikin cika shekaru 80 na Babanla Adinni na Egbaland, Cif Tayo Sowunmi, Daily Trust ta bayyana.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara bayyana cewa ya yi ayyuka a wurare daban-daban a da da kuma yanzu “kuma Alhamdulilah ya gode ma Allah da wannan gata da yayi masa”.

Shugaban darikar Tijjaniyya yaja hankali

Shugaban Darikar Tijjaniyyan ya kuma gargadi masu neman shugabancin kasar da su kasance cikin shiri don gudanar da ayyukan da zasu ciyar da kasa gaba.

Sunusi Lamido Sunusi - Shugaban darikar Tijjaniyya na kasa
Sunusi Lamido Sunusi – Shugaban darikar Tijjaniyya na kasa

Najeriya za ta fuskanci babban kalubale

Sunusi ya kuma kara bayyanawa a wurin taron cewa “Najeriya na rayuwa ne a cikin wani yanayi”. Ya ce kasar za ta fuskanci sosai a shekarar 2023.

Ga abinda ya ce:

“Maganan gaskiya, muna rayuwa ne a wani irin yanayi mai wuyan fassara. A shekarar 2015, mun fada cikin tafkeken rami mai zurfi. To a 2023, sai mun fada ramin da yafi na baya zurfi.

Kalubalen da ke gaban wadanda ke fafutukan neman kujeran shugabancin kasar, ina fata sun fahimci cewa matsalolin da za su fuskanta, sun banbantan da matsalolin da aka fuskanta a shekarar 2015 kuma dukkanmu za mu kasance a cikin shiri ga duk wani mawuyacin shawara da aka yanke. Idan haka ta kasance to fa kowa zai dandana a jikin shi .”


Abin da Najeriya ke bukata cimma nasara a matsayin ta na kasa

Da yake magana, Sunusi ya ce nasarar Najeriya ba wai ace karuwar masu shiga harkokin siyasa ba ne. Ya ce Babban abin da kasar ta fi bukata shi ne ’yan siyasa na gari, Limamai da Fastoci da Bishof wanda za su tashi tsaye su dinga tunatar da ’yan siyasa tsoron Allah.

Ya kara da cewa Najeriya na bukatar kwararrun masana da za su rika sukar manufofin ‘yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya wadanda za su yi magana a matsayin su na jagororin al’umma. A karshe ya ce:

Kowa yana da rawar da zai taka, kuma ya kamata mu yi kokarin ganin cewa mun taka rawar gwargwadon iyawar mu”.

A wannan karon ba zancen addini ko al’ada idan zabe ya zo, kowa yabi cancanta – Sunusi Lamido

Shugaban darikar Tijjaniyya na Nageriya, Khalifa Sunusi Lamido Sunusi, ya shawarci yan Nageriya da suyi rajistar zabe. Sannan kuma, su tabbata sun zabi mahimmai kuma kwararrun shugabanni, a duka mukaman siyasa, a zabe mai zuwa.

Sunusi Lamido Sunusi yayi kiran ne a Lakwaja ranar Lahadi, yayin gudanar da wani bikin maulidin shekara na duniya karo na hudu da aka shirya a Nageriya, domin girmama annabi Muhammadu S.A.W, me taken ” Maganin Matslar Dan Adam daga Annabi”

Malam Sunusi Lamido, wanda shine tsohon sarkin Kano, ya ja hankalin yan kungiyar dasu zabi muhimmin mutum wanda yake kuma gwararre ta ko wacce fuska. Batare da la’akari daga ina ya fito, menene addininsa, kokuma waccece jamiyyarsa ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labaunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe