27.1 C
Abuja
Monday, January 30, 2023

Abubuwa 3 na kamanceceniya da ke tsakanin Ummi Rahab da jarumar kudu, Regina Daniels

LabaraiKannywoodAbubuwa 3 na kamanceceniya da ke tsakanin Ummi Rahab da jarumar kudu, Regina Daniels


Ko ka taba ganin Regina Daniels da Ummi Rahab a tare? Idan da zaka kare musu kallo, zaka fahimci kamanceceniyar da suke yi da juna. Newsnownaija.com ta tattaro abubuwa uku na kamanceceniyar da ke tsakanin jaruma Ummi Rahab da Regina Daniels:

1. Jaruman guda biyu suna da kamanni sosai.

ummi and reg2
Jaruman guda biyu suna matukar kama da juna.

Idan da zakuyi dubi da hazukan jaruman guda biyu a talabijin, zakayi tsammanin suna da alaka ta yan uwantaka saboda irin kama da sukayi. Kama ta kyawun hallita da kuma kama ta hasken fata, dukka sunyi kama amma basu da alakar yan uwantaka.Regina yar asalin jihar Delta ce, ita kuma Ummi yar Kaduna.

2. Duka biyun sun fara wasan kwaikwayo tun suna yara.

ummi and reg3
Duka biyun sun fara wasan kwaikwayo tun suna yara.


Regina Daniels an haifeta a shekarar 2000, ta fara sana’ar wasan kwaikwayo lokacin tanada shekara 7.Fim din da ta fara bayyana shi ne “Marriage of Sorrow”.

Ita kuma Ummi an haifeta ne a shekarar 2004, ta fara wasan kwaikwayo a lokacin tana da shekaru 10 a duniya.Fim din da ta fara bayyana shi ne “Takwara Ummi”.

3. Suna da jibi a musulunci.

ummi and reg4
Dukan biyun su na da alaka da musulunci.

An haifi Ummi Rahab a cikin Musulunci a jihar Kaduna, hakan yana nufin tana da jibi da Musulunci ta hanyar haihuwa.

Ita kuma Regina Daniels ta dayan bangaren, ba’a haifeta cikin Musulunci ba, amma tayi aure a gidan Musulunci. Hakan yana nuna tanada alaka da Musulunci ta hanyar auratayya.

Wannan shi ne al’amarin, shin a ganinku wacece tafi wata kyau tsakanin su biyun?

Da dumin sa: Mawaki Lilin Baba yana shirye-shiryen auren jaruma Ummi Rahab

Fitaccen mawaki kuma jarumin shirin fim din Kannywood, Shu’aibu Ahmed Abbas, wanda kowa ya fi sani da Lilin Baba ya bayyana wa duniya cewa yanzu haka shirye-shiryen auren sa da jaruma Ummi Rahab ya kankama, Aminiya ta ruwaito.

Yayin tura sakon sa na yi wa jaruma Ummi Rahab fatan alheri a ranar da ta kara shekaru, ya tura sako gare ta kamar haka:

“Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki abar kauna ta, Ummi Rahab. Lallai kin kasance mutumiyar kirki ma’abociya zuciyar zinare.

“Ina tura miki sakon taya murnar zagayowar ranar da aka haife ki a daidai ranar da ki ka kara wata shekarar a rayuwar ki.”

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Daily Trust

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe