24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Bidiyon Rabiu Rikadawa da Hadizan Saima ya dauki hankulan jama’a da yawa a shafukan sadarwa

LabaraiAl'adaBidiyon Rabiu Rikadawa da Hadizan Saima ya dauki hankulan jama'a da yawa a shafukan sadarwa

Wani bidiyo na fitaccen jarumin barkwancin nan Rabiu Rikadawa da Hadizan Saima ya jawo kace-nace matuka a shafukan sada zumunta…

Idan ba a manta ba a shakaru biyu da suka gabata, BBC Hausa sun kawo wata hira da suka yi da jaruma Hadizan Saima, inda a cikin hirar BBC suka yi mata tambaya game da wanene bazawarin ta a masana’antar Kannywood.

Jarumar ta mayar da amsa taa hanyar fashewa da dariya tare da cewa sunan sa yana da tsada, sai dai tun a lokacin mutane sunyi ta canki-canka akan wanene wannan bazawari nata, inda mafi yawanci ake hasashen jarumi Rabiu Rikadawa, sai dai babu tabbas kan wannan hasashe.

Mutane sun dogara da yawan fitowar Rikadawa da Hadiza a fim

Yawancin masu hasashen sun dogara ne da yawan fitowar su a fina-finai tare da kuma kyakkyawar alakar dake tsakanin su.

Rabiu Rikadawa
Rabiu Rikadawa – Hoto BBC Hausa

A ‘yan kwanakin nan wannan batu ya sake dawowa sabo a yayin da aka tsinkayi wani bidiyo na jaruman biyu suna bin wata wakar soyayya da ke tashe mai suna ‘Lamaba” suna yiwa juna kallon soyayya.

Da ganin wannan bidiyo sai fa kowa ya fara tofa albarkacin bakin sa kan wannan hadi gami da gaskata wancan hasashen da aka dinga yi a baya.

Ba wannan ne karo na farko da jaruman Kannywood suka saba yin irin wannan bidiyo ba

To sai dai irin wannan bidiyo wani abu ne da ya zama ruwan dare a masana’antar ta Kannywood, inda namiji da mace kan bi wakar soyayya koda kuwa babu komai a tsakanin su domin jan hankalin jama’a da tallata waka ko fim.

Sai dai wannan bidiyo na Rikadawa da Hadizan Saima ya dauki hankulan mutane matuka musamman ma idan aka yi la’akari da yawan shekarun su da kuma wancan hasashen da ake yi musu da, da wannan muke cewa idan hasashen ya zama gaskiya, muna fatan Allah ya tabbatar da alkhairi.

Jaruman Kannywood sun cika da murna kan yabon da Sheikh Abubakar Abdulsalam ya yi musu

A ranar Asabar 23 ga watan Oktobar nan ne muka kawo muku wata lakca da Sheikh Abubakar Abdulsalam Baban Gwale yayi kan tarbiyyar yara, inda a ciki da yazo magana kan kallon TV ya yi wani tsokaci kan fina-finai.

Malamin ya bayyana cewa a duk masana’antun shirya fina-finai na duniya babu masana’antar da ta kai ta Kannywood tsafta domin kuwa har yanzu sune basu yadda da taba mace daidai ba ne.

Wannan magana da Shehin Malamin ya yi ta yiwa jaruman Kannywood dadi, domin ko ba komai sun samu karin irin Malaman dake fadar alkhairin su komai kankantar sa, inda suka dinga wallafa tsakuren lakcar daidai inda ya yabe sun suna godiya da nuna jin dadin su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe