36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Bi’izinillahi duk dan takarar da Buhari ya daga hannun sa sai mun kayar da shi – Sheikh Bello Yabo

LabaraiBi'izinillahi duk dan takarar da Buhari ya daga hannun sa sai mun kayar da shi - Sheikh Bello Yabo

Sheikh Bello Yabo ya bayyana cewa idan zabe 2023 ya zo, duk dan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsayar sai sun kada shi…

A daidai lokacin da aka fara buga gangar siyasa a Najeriya, ‘yan siyasa da dama sun fara fitowa suna baja kolin kansu ga al’ummar Najeriya, musamman ma wadanda suke da burin fitowa takarar shugaban kasa.

Zuwa yanzu dai an samu maanyan ‘yan siyasa da dama da suka fito suka nuna ra’ayinsu na fitowa takarar shugaban kasa, wadanda suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagos, kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha da dai sauran su.

Sheikh Bello Yabo ya caccaki ‘yan siyasa

A wannan karon shahararren Malamin nan ne na addinin Musulunci na jihar Sokoto, Sheikh Bello Yabo ya fito yana caccakar ‘yan siyasar, da kuma nuni ga al’umma akan irin shugaban da ya kamata al’umma su zaba.

Sheikh Bello Yabo
Sheikh Bello Yabo

A cikin maganganun na Malamin da muka ci karo da su a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Sheikh Al-Bani Sheikh Jaafar ya bayyana cewa, duk wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tsautsayin tsayarwa takara sai sun kayar da shi, ga dai kadan daga cikin abinda Malamin ya ce:

“Yanzu an kusa kada gangar siyasa, gwamnatin da ta wuce ta PDP karkashin jagorancin Goodluck Jonathan, ta karye ne saboda sun kyale ana kashe mutane.

“To abinda ya ci waccan gwamnti haka ita ma wannan gwamnatin zai ci ta, saboda haka sun riga sun yi hasashen hakan.

“Bari na fadi wani sirri wanda da yawan mutane basu san da shi ba, a baya ana rudar mutane ana cewa lokacin da Buhari ya hau mulki wasu kananan hukumomi a jihar Borno suna hannun Boko Haram, Wallahi karya ne. Lokacin da Buhari ya hau mulki babu karamar hukuma daya dake hannun Boko Haram.

“Lokacin da zabe ya zo kusa a wancan lokaci, aka ga cewa babu wata mafita, sai aka yiwa Jonathan magana, aka ce masa akwai wasu garuruwa a hannun Boko Haram, saboda haka zabe ba zai yiwu ba a wannan yankin, koda ma a ce ya yiwu ba za a zabe mu ba, saboda haka ka tashi kayi wani abu.

Lokacin da Buhari ya hau kujera babu karamar hukuma daya dake hannun Boko Haram a jihar Borno

“Lokacin da aka saka zabe cikin sati shida duka kananan hukumomin dake hannun Boko Haram aka karbo su, lokacin da Buhari ya hau mulki babu karamar hukuma ko daya dake hannun Boko Haram.

“Yanzu wasan kwaikwayon da za a sake mana kenan, bayan sun kyale an kashe mutane an salwantar da dukiyoyin al’umma, sai aka fara tura ‘yan sanda, ba wai sojoji ba.

“Kun san dalilin tura sojoji da aka yi jihar Sokoto, shine saboda zabe ya zo kusa, sun san in dai aka kai lokacin zabe haka babu wanda zai zabe su. Buhari ya gama faduwa, kuma ba Buhari ba, duk wanda Buhari ya daga hannunsa sai mun kada shi, Bi’izinillahi.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Sokoto, inda ya kaddamar da kamfanin siminti a jihar.

Idan har Rarara na raye kamata yayi ya fito yayi wakar zuwan mai hula Lagos – Sheikh Bello Yabo

Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Bello Yabo ya caccaki shahararren mawakin siyasar nan na Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara, sakamakon shiru da ya fito yayi a wannan lokaci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa ‘yan Arewa laifi.

Malamin ya ce a lokacin mulkin PDP na Goodluck Jonathan, Rarara ya sha yin wakoki na cin mutunci kan yadda Jonathan ke tafiyar da mulkin shi a wancan lokacin, inda a lokacin mutanen Arewa dadi suka dinga ji suna yaba masa, sai dai a wannan karon kuma da abin ya dawo kan shugaba Buhari yayi shiru da bakin sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe