24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Kotu ta yanke wa Sadiya Haruna hukuncin watanni 6 a gidan yari saboda batanci ga Isah A. Isah

LabaraiKannywoodKotu ta yanke wa Sadiya Haruna hukuncin watanni 6 a gidan yari saboda batanci ga Isah A. Isah

A ranar Litinin wata kotun majistare da ke filin jirgin Mallam Aminu Kano ta yanke wa wata fitacciyar jarumar Kannywood kuma sananniya a Instagram, mai suna Sadiya Haruna hukuncin wata shida a gidan yari akan cin zarafin wani jarumin Kannywood, mai suna Isah Isah da tayi, Daily Nigerian ta ruwaito.

An samu labarin yadda jarumar ta zage Isah a Instagram sannan ta yada a kafafen sadarwa, inda tayi amfani da kalamai marasa dadi, hakan ya tunzura shi ya dauki matakin da ya dace.

sadiyya haruna 1
Kotu ta yanke Sadiya Haruna hukuncin watanni 6 a gidan yari saboda batanci ga Isah A. Isah

Daily Nigerian ta tattaro bayanai akan yadda jarumar a wani bidiyo da ta wallafa a shafin ta na Instagram ta zargi Isah da yin auren mutu’a da ita, yayin da ya sadu da ita ta baya ba da son ranta ba.


Haka zalika, ta kira shi da mazinaci, dan luwadi, shege da sauran munanan maganganu.
An gurfanar da ita ne a gaban kotu a ranar 16 ga watan oktoban 2019, inda ake tuhumarta da bacin suna wanda yaci karo da sashi na 391 na kundin tsarin shari’a.


Daga karshe alkalin kotun Majistaren Muntari Dandago ya yanke mata hukuncin wata shida a gidan yari ba tare da tara ba.

Daga karshe, Sadiya Haruna ta hakura da zaman Kano bayan an kusa watsa mata ‘Acid’

Fitacciyar mai sayar da maganin mata a garin Kano, ‘yar asalin Maiduguri, Sadiya Haruna ta bayyana shirin ta na komawa Jihar Borno, tushen ta.

Tun ranar Juma’ar da ta gabata ake ta tirka-tirka har kafafen sada zumuntar zamani suka dauki zafi bayan Sadiya Haruna ta wallafa bidiyon ta tana ihu tare da kuka yayin da take.

A cikin bidiyon ta bayyana sanye da wani hijabi wanda ta yi cikin mota tana neman taimako inda tace bata san inda dan’uwanta yake ba.

Sadiya Haruna ta shaida yadda wasu maza suka bi ta zasu watsa mata ‘acid’ bayan ta tashi daga shagonta ta zarce siyayya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe