34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Tun shekarar 2011 ake tuhuma ta da hannu a rikicin Boko Haram – Ali Modu Sharif

LabaraiTun shekarar 2011 ake tuhuma ta da hannu a rikicin Boko Haram - Ali Modu Sharif
  • Ali Modu Sharif ya musanta zargin da ake masa akan alakar sa da Boko Haram
  • Jami’an tsaro sun matsa masa da bincike tun saukar sa akan karagar mulki
  • Sunan sa baya cikin jerin sunayen da daular Dubai ta fitar

Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali-Modu Sheriff, ya karyata zargin da ake masa na cewa yana da alaka da ‘yan ta’addan Boko Haram, ya kara da cewa jami’an tsaro sun matsa masa da bincike tun bayan da ya bar karagar mulki a shekarar 2011.

Daraktan kungiyar Ali-Modu Sheriff Campaign Organisation, Victor Lar, ya musanta zargin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Lahadi a garin Abuja.

Ya ce Mista Sheriff, wanda ya kasance kan gaba wajen neman kujerar shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), kuma ya kasance tsohon gwamnan Borno da ya yi wa’adin mulki har sau biyu kuma tsohon Sanata, ba shi da wata alaka da kungiyar Boko Haram.

Sunan sa baya cikin jerin sunayen da Daular Larabawa ta fitar

“Sunan Sheriff ba ya cikin jerin sunayen masu daukar nauyin Boko Haram da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta fitar, tun bayan da ya bar mulki a shekarar 2011 hukumomin tsaro ke bincike a kansa amma har yanzu basu same shi da laifin komai ba.

“Idan da yana da hannu, da an dade da kama shi ko kuma da asirinsa ya tonu ya bayyana a fili kowa ya gani. Saboda haka, ina kalubalantar duk wanda ke da bayanin cewa yana da tabbaci da sa hannun sa to ya fito ya bayyana ,” in ji shi.

Mista Lar ya kuma bayyana cewa zarge-zargen da ake tuhumar Sheriff da su idan ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa, to fa zai kasance da tangarda saboda yana da shari’a da kararraki da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, wanda hakan kuma ba gaskiya ba ne.

Sharif bai da matsala da EFCC

“Idan mutum yana da shari’a da EFCC to fa hakan yana nufin a gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma a tuhume shi. wanda Sharif ba shi da daya daga cikin wanan matsalar, wadanda ake zargi su ne za su je EFCC,” in ji Mista Lar.

Don haka ya yi watsi da zarge-zargen da ake ma shugaban nasa, yana mai cewa, rashin fahimta shi ya kawo hakan da kuma masu yawo suna yadawa.

Mutane na ta cece-kuce bayan an jiyo Rochas Okorocha na jawo ayar Al-Qur’ani mai girma a wajen kamfen din shi

Idan ba a manta ba, Okorocha ya bayyana ra’ayin sa na takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC a wata takarda wacce ya tura wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Yayin jawabin sa, an ga sanatan yana janyo aya daga cikin Al’Qur’ani mai girma inda yace shi dan takara ne mai adalci kamar yadda Allah ya umarci yin adalci cikin Suratul Nahli.

Ya bukaci duk masu sauraron sa da su zabe shi don zai samar da sabuwar Najeriya. Okorocha wanda yanzu haka sanata ne mai wakiltar Imo ta yamma ya sha cece-kuce bayan janyo ayoyin Qur’ani.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe