27.4 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Da dumin sa: Mawaki Lilin Baba yana shirye-shiryen auren jaruma Ummi Rahab

LabaraiKannywoodDa dumin sa: Mawaki Lilin Baba yana shirye-shiryen auren jaruma Ummi Rahab

Fitaccen mawaki kuma jarumin shirin fim din Kannywood, Shu’aibu Ahmed Abbas, wanda kowa ya fi sani da Lilin Baba ya bayyana wa duniya cewa yanzu haka shirye-shiryen auren sa da jaruma Ummi Rahab ya kankama, Aminiya ta ruwaito.

Yayin tura sakon sa na yi wa jaruma Ummi Rahab fatan alheri a ranar da ta kara shekaru, ya tura sako gare ta kamar haka:

“Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki abar kauna ta, Ummi Rahab. Lallai kin kasance mutumiyar kirki ma’abociya zuciyar zinare.

“Ina tura miki sakon taya murnar zagayowar ranar da aka haife ki a daidai ranar da ki ka kara wata shekarar a rayuwar ki.

“Ina fatan yau za ta zama ranar murna a gare ki tare da farin ciki. Ina jin dadin ganin yadda kika samu ci gaba a rayuwar ki. Ina fatan Allah ya albarkaci rayuwar ki.”

lilin baba
Da dumin sa: Mawaki Lilin Baba yana shirye-shiryen auren jaruma Ummi Rahab

Can a karshen wallafar tasa sai ya ce:

“Na kusa yin Wuf da ke in sha Allah!”

A karkashin wallafar, jarumar ta nuna jin dadin ta dangane da wallafar ta shi inda ta yi masa tsokaci.

Kamar yadda ta yi masa martani inda ta ce:

“Ina mika godiya ta abin kauna ta. Lallai kai ne a gaba cikin jerin mutane, mijina na nan gaba. Na kosa in ga ranar. Allah ya nuna mana.”

Ummi Rahab: Adam A Zango ya saba auren yaran sa mata ni ba irin su ba ce

Bayan kura ta lafa a dambarwar dake tsakanin jarumi Adam A Zango da ‘yar dakin sa Ummi Rahab, a karon farko jarumar ta yi magana tun bayan fara dambarwar, inda a jiya ta samu tattaunawa da jaridar Daily Trust kan abin da ke tsakanin ta da Adam A Zango.

A cikin hirar Ummi Rahab ta bayyana cewa har yanzu tana daukar Adam A Zango a matsayin Uba, kuma tana girmama shi, amma kowa ya kama hanyar sa ba batun sake tafiya tare.

Haka zalika tayi karin haske kan cire ta da yayi daga cikin shirin “Farin Wata Sha Kallo”, inda ta bayyana yana da damar saka duk wanda ya so a fim din sa da cire duk wanda ya so ba ta da matsala da hakan, amma ta danganta hakan da kishin kula samarin da take, ya kuma yi kokarin hana ta taki hanuwa yasa shi yayi abinda yayi.

Ummi Rahab ta bayyana cewa ita baza ta iya auren shi ba tunda yana matsayin uba a wajenta, inda tace shi kuma ya gaza fahimtar hakan, ta ce ya saba da auren yaran sa mata da yake fim da su, sai dai ita ba haka take ba tana da ikon yin yadda ta so da rayuwar ta, indai tsarin bai sabawa shari’a ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Source: Daily Trust

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe