24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Za mu kammala aikin titin jirgin kasa na Kaduna zuwa Kano kafin Buhari ya sauka a mulki – Amaechi

LabaraiZa mu kammala aikin titin jirgin kasa na Kaduna zuwa Kano kafin Buhari ya sauka a mulki - Amaechi
  • Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa yana jin dadi a duk lokacin da ya ji jama’a na yaba irin kokarin da ya ke yi na ayyuka
  • Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya jaddada cewa za suyi kokari ganin layin titin jirgin kasa ya fara aiki nan ba da jimawa ba
  • Ya umurci wadanda aka ba kwangilar da suyi amfani da injuna na gida da na waje don ganin aikin bai ci lokaci ba

Ministan Sufuri kuma Dan Amanan Daura, Rotimi Amaechi, ya ce nadin da aka yi masa a matsayin Dan Amanan Daura ma’ana “Amintaccen dan Daura” kadan ne da ga cikin ayyukan da ya ke yiwa jama’a.

Amaechi, wanda aka yi masa wankan sarauta a ranar Asabar din data gabata a fadar Sarkin Daura, ya ce abun yana matukar sa shi farin ciki idan ya ga jama’a suna yaba kyawawan sauye-sauyen da aka samu a harkar sufuri wanda ke karkashin ikonsa.

Ya je rangadin aiki

A rahoton da jaridar Leadership ta ruwaito, ministan, wanda ya bayyana hakan a yayin wani rangadin aiki da ya je, sai dai ya danganta hakan ne dalilin kudade da ake fitar wa don aikin.

Amaechi ya ce sakamakon tsaikon da aka samu wajen karbo bashi daga kasar China, a halin yanzu gwamnatin tarayya ce ke daukar nauyin aikin daga cikin kasafin kudin shekara da aka fitar.

Rotimi Amaechi - Ministan Sufuri
Rotimi Amaechi – Ministan Sufuri – Hoto Daily Post

Ya kuma bukaci ’yan kwangilar da aka dauko daga kasar China da su karkasa aikin zuwa rukuni-rukuni, su sa ma’akata su yi aiki lokaci guda, su kuma kawo karin injuna da kuma yin amfani da abubuwan cikin gida don ganin an kammala aikin akan lokaci.

Kalubalen daya fuskanta

Dangane da wasu kalubalen da ya fuskanta a lokacin da yake gudanar da ayyukan jiragen kasa a fadin kasar nan, ministan ya ce:

“Ban taba musanta cewa ba ma fuskantar kalubalen rashin kudi ba kuma hakan ya faru ne saboda tabarbarewar tattalin arziki.

“Mutanen da suka zo da ga China don yin kwangilar ba su samu yadda suke so ba, shi yasa har yanzu ba mu gama yanke shawaran karban bashi ba don karasa aikin Kano zuwa Kaduna, shiyasa kawai muke amfani da kasafin kudaden da kasa ta fitar.

Da yake karin haske game da aikin da kuma manufar kammala aikin, ya ce:

“Ina da tabbacin cewa idan muka ba su kudade, dole ne su kammala aikin. Dole ne su yi abin da aka tsadance za su yi. Tattaunawar da muka yi da su ita ce, dole ne za su raba wannan aikin zuwa kashi-kashi saboda ya kasance kowa ya gama aikinsa lokaci guda. Idan sun yi haka, na tabbata kafin watan Mayu, 2023 za a fara hada hadan kasuwanci a kan hanyar.

Za ayi jigilar mutane da kaya

“Za a yi amfani da hanyar ne wajen jigilar fasinjoji da kaya. Daya daga cikin cibiyoyin tattalin arziki a kasar nan su ne Kano da Legas. Wannan shine dalilin da ya sa wannan harkar zata zamo hanya mafi dacewa ga tattalin arziki.

“Ayyukan tattalin arzikin da ke gudana a Kano ana iya jigilan su zuwa Legas haka ma wadanda suke aiki a Legas za su iya kai kayayyakinsu zuwa Kano. Wannan zai samar da ayyukan yi kuma tsadar filaye a nan ba zai zama kaman na da ba.”

Hotuna da bidiyon yadda aka gudanar da bikin nadin sarautar Amaechi a garin Daura

Mahaifar Buhari wato Daura ta cika da annashuwa yayin da aka ba wa Rotimi Amaechi saurautar gargajiya, bidoyon da ya bazu a yanar gizo ya nuna lokacin da yake tafe a kan doki misalin karfe 11:11 na safiyar ranar Asabar, 6 ga watan Fabrairun 2022, Legit.ng ta ruwaito.

Sarkin Daura, mai martaba Faruk Umar Faruk, ya nada Rotimi Amaechi a matsayin ‘Dan Amanar Daura a ranar Asabar. Sarautar gargajiyar mai taken ‘Dan amanar masarautar Daura da aka ba shi yana nuni da yaba wa kokarin Amaechin wajen kawo ci gaba ga masarautar.

Yayin nuna cancantar mukamin ga Amaechi, Sarkin ya bayyana dalilin da yasa ya ba shi sarautar kawai saboda matukar kwazon sa ne.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe