24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Wata budurwa ‘yar Ghana mazauniyar Canada ta ba da labarin gwagwarmayar da ta sha kafin samun aikin yi

LabaraiWata budurwa 'yar Ghana mazauniyar Canada ta ba da labarin gwagwarmayar da ta sha kafin samun aikin yi


Wata budurwa ‘yar Ghana mai suna Lissa Appiah ta shiga shafukan sada zumunta inda ta ba da labarin halin da ta shiga na tsanani da kuma jajircewa da ta yi.

A wani rubutu da budurwar ta wallafa a shafin ta na LinkedIn, ‘yar kasar Ghanan mazauniya kasar Canada ta bayyana cewa ta fuskanci kalubale da dama a rayuwarta kafin ta mallaki nata kasuwanci.

Lady gets dream job
Wata budurwa ‘yar Ghana mazauniyar Canada ta ba da labarin gwagwarmayar da ta sha kafin samun aikin yi

Budurwa Lissa ta bayar da labarin cewa kafin ta sami gurbin karatu don yin karatun digiri na biyu, ta fuskanci jarabawa ta daban-daban har guda hudu daga wurin tallafin karatu.
Sai dai ta samu nasarar kammala digirin ta na biyu kuma a yanzu ta nemi aikin horarwa kuma hakan ya zo da nasa kunshin na kin amincewa.

“An ƙi ni daga ya kai sama da sau 10 kafin in samu abinda na ke bukata har in samu damar fara aiki na,” ta rubuta.

A karshe budurwar ta bayyana cewa a duk tsawon wannan aiki, an hana ta karin girma sama da sau 20 har zuwa lokacin da ta samu nasara kuma tun daga wannan lokacin ta sami karin girma daban-daban guda biyar a cikin shekaru takwas.

“An hana ni damar karin girma sama da sau 20 kafin in fara haɓakawa na farko – yanzu an ƙara mini girma sau 5 a cikin shekaru 8.”

Lissa ta ci gaba don ƙarfafa guiwar mutane su yi aiki tukuru a koyaushe a matsayin jagora don samun ingantacciyar dama da amincewa da tsarin.

Budurwa ta kwashe saurayinta da mari har sau 2 saboda ya nuna yana son aurenta a bainar jama’a

Wani saurayi da yayi yunkurin bawa budurwar shi mamaki wajen neman aurenta, amsar da ta dawo mishi da ita ba ta yi masa dadi ba, yayin da budurwar ba wai taki amincewa ba ne kawai, ta mayar da martani da duka ne.

Wani mai amfani da shafin sadarwa na Twitter, mai suna @EazyKel_who yaa wallafa bidiyon yadda wannan lamari ya faru a shafinsa, inda ya caccaki mutumin kan dalilin da ya sanya ya nemi auren budurwar tashi a bainar jama’a.

Neman auren bai yiwa saurayin yadda yake so ba

Yayin da aka nuno saurayin ya durkusa a gaban budurwar, ga kuma cake a kan tebur inda budurwar take zaune, an gano budurwar ta tashi tsaye ta kwashe shi da mari, inda take tambayar shi dalilin da ya sanya shi ya zo wajen.

Duk da kokarin da mutane suka din yi wajen ganin sun shawo kan budurwar, budurwar ta kara kwashe saurayin da mari a karo na biyu a yayin da yake tsugunne a gabanta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe