29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Ma’aikatan lafiya na shirin maka Sheikh Abdallah Gadon Kaya a kotu idan bai janye kalaman sa na cewa suna zina a asibitoci ba

LabaraiMa'aikatan lafiya na shirin maka Sheikh Abdallah Gadon Kaya a kotu idan bai janye kalaman sa na cewa suna zina a asibitoci ba

Shahararren Shehin Malamin nan mai tsage gaskiya komai dacin ta kan al’amuran dake faruwa a cikin al’umma, wato Sheikh Abdallah Gadon Kaya, wanda sau da dama irin wannan fadar gaskiya tasa kan jawo masa tsangwama daga ba’arin da ya magantu a kan su.

A wannan karon ya taboma’aikatan asibiti, inda ya bayyana wasu abubuwa da yace suna faruwa a asibitocin mu na Allah wadai.

Da dadewa Malamin yayi wata lakca da ta fayyace irin abin ashshan da mata masu aikin kwana a asibiti ke yi, wasu matan aure ne, inda wannan lakca tashi tayi ta yawo a shafukan sada zumunta.

Ga kadan daga cikin abinda Malamin ya ce

“Ana yin zina da mata da suke aiki na hukuma, sai wadanda Allah ya tsare, wasu a cikin ma’aikatar saboda rauni irin na mace, wasu kuma shugabannin ma’aikatun ne suke amfani da girman kujerarsu su lalata matan da suke karkashin su.

Sheikh Abdallah Gadon Kaya
Sheikh Abdallah Gadon Kaya

“A ma’aikatun lafiyar nan kamar sauran ma’aikatu suma suke, su muna buga misali da sune, saboda mutum yana samun kwanciyar hankali ya kyale matarsa ta tafi taje tana aikin dare. Tsari ne ba na Musulunci ba, sai a hada mace da namiji aikin kwana a ofishi daya.

“Tana aikin kwana wani saurayi balagagge shima yana aikin kwana, zaka ganta daga ita sai ‘yar fangalalliyar riga, kuma a daki daya, su tura kofa su rufe, karfe uku na dare babu kowa, daga su sai shaidan, kana can gida kana ta birgima sauro na ta cizon ka, kana cewa ai Madam tana aikin kwana.

Shugaban ma’aikatan lafiya ya caccaki Sheikh Abdallah Gadon Kaya

To sai dai wannan magana ta jawo ma’aikatan lafiya reshen jihar Kano karkashin jagorancin shugaban kungiyar su Kwamaret Ibrahim Mai Karfi Muhammad, sunyi kira ga Malamin da ya gaggauta janye kalaman sa ya kuma basu hakuri ko kuma su dauki mataki.

Mai karfi ya bayyana haka a wata hira da yayi da Jarida Radio, inda ya ce:

“Wannan wani babban abin tashin hankali ne ya same mu, da kuma al’ummar jihar Kano, da al’ummar Musulmai baki daya. Akwai wani Malami da ya saki wani abu a kafafen sadarwa, wanda yake gabatar da wani mummunan zargi ga ma’aikatan lafiya, na magana ta zina, Allah ya kiyaye mu.

“A cikin maganganunsa yana cewa ma’aikatan lafiya suna kwana a daki daya, har yana kawo wani mummunan hasashe na cewa wani mummunan abu yana faruwa tsakaninsu.

“Abu na farko muna so mu bawa mutanen mu hakuri, na wannan mummunar kama da aka danganta su da ita, sannan abu na biyu muna kira ga wannan Malami da ya gaggauta janye wannan magana da yayi, sannan ya bawa mutanen mu da al’ummar jihar Kano hakuri.

Muna goyon bayan hukuncin Malam – Aisha Buhari ta goyi bayan Sheikh Abdallah kan a yankewa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta sanya baki dangane da maganar hukuncin da ya kamata a yankewa Abdulmalik Muhammad Tanko, shugaban makarantar su Hanifa Abubakar, wacce ya sace ta ya kuma yi mata kisan gilla.

Matar shugaban kasar ta bayyana ra’ayinta a shafin ta na Instagram a ranar Litinin 24 ga watan Janairu, inda ta nuna goyon bayan ta akan a kashe Abdulmalik Tanko kamar yadda ya dauki rayuwar Hanifa.

Aisha ta bayyana hakane sakamakon wani bidiyo na Shahararren Malamin addinin Islama din nan na jihar Kano, Sheikh Dr Abdallah Gadon Kaya, wanda ya bukaci a yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe