24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

‘Yan sandan Kaduna sun kama jami’in KASTELEA da ya yi wa direban duka, ya kashe shi har lahira

Labarai'Yan sandan Kaduna sun kama jami’in KASTELEA da ya yi wa direban duka, ya kashe shi har lahira

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun kama wani jami’in hukumar kiyaye zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kaduna wanda ake zargi da lakaɗawa wani direban mota dukan tsiya har lahira a hanyar Ali Akilu, a cikin kwaryar birnin jihar aUngwan Sarki ranar Juma’a.

Kamen ya biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar Mudassiru Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammad Jalige, ya ce.

'Yan sandan Kaduna sun kama jami’in KASTELEA da ya yi wa direban duka, ya kashe shi har lahira
‘Yan sandan Kaduna sun kama jami’in KASTELEA da ya yi wa direban duka, ya kashe shi har lahira

Unguwan Sarki tana cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Lamarin dai kamar yadda wani mutum ya shaida, ya faru ne da karfe huɗu na yamma, inda ya kai ga yin kaca-kaca a unguwar Ungwan Sarki da ke jihar.

An tattaro cewa an kashe direban ne bayan wata hatsaniya da jami’in kula da ababen hawa. Shaidar ya ce direban ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu a kai, inda ya kara da cewa dan sandan ya bugi marigayin da sanda a yayin gardama.

Kakakin ‘yan sandan, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da umarnin kama jami’in kula da ababen hawa da ke da alhakin faruwar lamarin.

“An samu hatsaniya tsakanindan KASTLEA da wasu direbobi. Sun yi masa duka aka garzaya da shi asibiti inda ya rasu. Don haka direbobin suka yanke shawarar tare babbar hanyar domin nuna fushin amma mun hana su,” ya kara da cewa.

Jalige ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin da nufin gano musabbabin faruwar lamarin.

‘Yan sanda sun cafke wasu matasan da suka kashe budurwar domin yin tsafin kudi da ita

Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu matasa uku da laifin kashe wata budurwa domin yin tsafin kudi da ita a jihar Ogun.

An kama su ne bayan wani jami’in tsaro ya gansu suna kona wani abu da ake tuhuma wanda ya zama kan mutum a cikin wata tukunya.

A halin yanzu, jami’an ‘yan sanda na ci gaba da neman mutum na hudu wanda ake zargi da zama saurayin wacce aka kashe
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wasu matasa hudu da laifin kashe budurwar daya daga cikin matasan saboda su yi tsafin kudi da ita.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe