27.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Najeriya za ta girgiza bayan yankin kudu ta yanke hukunci a kan takarar shugabancin kasa na 2023 -Wike

LabaraiNajeriya za ta girgiza bayan yankin kudu ta yanke hukunci a kan takarar shugabancin kasa na 2023 -Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Najeriya za ta girgiza ranar da yankin kudancin ƙasar nan zai bayyana ƙudurin sa kan zaben shugaban ƙasa na 2023.

Hakan dai ya zo ne kamar yadda gwamnan ya ce jam’iyyar PDP ba za ta baiwa duk wani ɗan takara da zai yi amfani da muradin ‘yan tsirarun masu hannu da shuni a Najeriya kaɗai ba.

Najeriya za ta girgiza bayan yankin kudu ta yanke hukunci a kan takarar shugabancin kasa na 2023 -Wike
Najeriya za ta girgiza bayan yankin kudu ta yanke hukunci a kan takarar shugabancin kasa na 2023 -Wike

Wike, duk da haka, ya lura cewa wasu ‘yan siyasa masu ra’ayin mazan jiya wadanda ba za su yi amfani da muradin mutane da yawa ba, maimakon sha’awar wasu masu hannu da shuni sun riga sun ƙulla makirci don zama ‘yan takara.

Kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Kelvin Ebiri ya fitar, a garin Fatakwal ranar Asabar, Wike ya bayyana haka a wani gagarumin liyafa da al’ummar ƙabilar Kalabari suka shirya domin karrama shi a ƙaramar hukumar Asari Toru.

An bai wa gwamnan sarautar gargajiya ta Se- Ibidokubo na ƙasar Kalabari (Mai kyautatawa mutanen Kalabari) kuma Amayanabo na Abonnema, Sarki Gboko Desreal Bob-manuel ne ya yi wa gwamnan sarauta.

Ya ce, “Ranar da Kudu za ta yi magana Nijeriya za ta girgiza. Mun yi imani da haɗin kan ƙasar nan, amma babu wanda zai iya yi mana barazana; kada wani ya yi mana barazana. Mun yi imani da hadin kan Najeriya da hadin kan Najeriya dole ne a samu ci gaba.”

Ya shaida wa mutanen Kalabari cewa sun yi kyau ta fuskar kaunar junansu da kuma yin aiki tare.

Najeriya ta zama kasa ta 1 a Afrika da tafi noman shinkafa, inda ta zama kasa ta 14 a duniya baki daya

A kididdigar da Ma’aikatar Noma ta kasar Amurka (USDA) ta fitar a shekarar 2021, ta nuna cewa yawan noman shinkafa a duniya daga shekarar 2020 zuwa 2021 ya kai tan miliyan 503.17, inda ya ninka da kimanin tan miliyan 1.97 fiye da shekarar da ta gabata.

A shekarar 2020 dai yawan noman shinkafar yana kan tan miliyan 496.40. Inda a shekarar 2021 kuma ya kai tan miliyan 503.17, inda aka samu karin kimanin tan miliyan 6.77, kimanin kashi 1.36% a fadin duniya, sai dai kuma har ya zuwa yanzu ba a fitar da kididdigar ta wannan shekarar ba.

A rahoton da shafin yanar gizo na World Agricultural Production.com ya wallafa, sun lissafo kimanin kasashe 90 a duniya da suke noman shinkafa, inda kasar Cina ta zama kasa ta daya a duniya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe