36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Zazzabin Lassa: NCDC ta ce mutane 40 sun rasu, ma’aikatan lafiya 4 sun kamu da cutar a watan Janairu

LabaraiNajeriyaZazzabin Lassa: NCDC ta ce mutane 40 sun rasu, ma’aikatan lafiya 4 sun kamu da cutar a watan Janairu

Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta ce mutane 40 ne suka rasu sakamakon zazzaɓin Lassa a watan Janairu, inda ta kara da cewa ma’aikatan lafiya hudu sun kamu da cutar bayan ɓullar cutar zazzaɓin Lassa a ƙasar.

Hukumar NCDC, ta shafin ta na yanar gizo da aka tabbatar, ta bayyana hakan a safiyar Lahadi, inda ta ce a halin yanzu tana raba kayayyakin jinya ga jihohi da cibiyoyin jinya.

Zazzabin Lassa: NCDC ta ce mutane 40 sun rasu, ma’aikatan lafiya 4 sun kamu da cutar a watan Janairu
Zazzabin Lassa: NCDC ta ce mutane 40 sun rasu, ma’aikatan lafiya 4 sun kamu da cutar a watan Janairu

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa zazzaɓin Lassa zazzaɓi ne na jini da beraye ke yadawa. An san shi tun shekarun 1950, amma ba a gano cutar ba sai a shekarar 1969, lokacin da ma’aikatan jinya biyu ‘yan mishan suka mutu daga cutar a garin Lassa na Najeriya.

An samo shi galibi a Yammacin Afirka, ya na da yuwuwar haifar da mutuwar dubunnan mutane. Ko bayan murmurewa, ƙwayar cutar ta kasance a cikin ruwan jiki, gami da maniyyi.

Ƙasashe maƙwabta kuma suna cikin haɗari, yayin da kwayar cutar ta Lassa, ” ɓera me nono” (Mastomys natalensis) ke yaɗuwa a duk yankin.

A cewar hukumar, a watan Janairu, mutane 40 da suka mutu da kuma 981 da aka samu a watan Janairun 2022 sun kasance a faɗin kananan hukumomi 43 a cikin jihohi 14.

Hukumar kula da lafiyar jama’a ta ce “Daga mako na 1 zuwa mako na 4, 2022, an samu rahoton mutuwar mutane 49 tare da adadin wadanda suka mutu ya kai kashi 19.0 cikin ɗari”.

A dunƙule, a shekarar 2022, Jihohi 14 sun sami aƙalla guda ɗaya da aka tabbatar a kananan hukumomi 43. A cikin dukkan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, kashi 82% sun fito ne daga jihohi kamar haka – Ondo (30%), Edo (27%) da Bauchi (25%).

Mafi girman rukunin shekarun da abin yafi shafa shi ne masu shekaru 21-30.

Cibiyar ta kuma lura da cewa, “ma’aikatan kiwon lafiya hudu sun kamu da cutar ya zuwa yanzu, 233 sun kamu da cutar, 617 kuma an gano wadanda suka kamu da cutar yayin da 968 aka jera don bin diddigin.”

Hukumar ta ƙara da cewa jihohin da ake zargin sun kamu da cutar sun hada da; Edo, Ondo, Bauchi, Benue, Oyo, Taraba, Ebonyi, Kogi, Kaduna, Katsina, Ebonyi, Plateau, Cross River, Borno, Anambra, Bayelsa, Jigawa, Kebbi, Ogun, Kwara, Lagos, Delta, Gombe, FCT, Nasarawa , Rivers da kuma Enugu.

Hukumar NCDC ta ce cutar zazzaɓin Lassa yana faruwa ne ta hanyar kwayar cutar RNA da ke daure da juna kuma cuta ce da ake yaɗawa.

“Don haka ya kamata ma’aikatan kiwon lafiya su daina nuna shakku kan cutar zazzaɓin Lassa, su yi taka-tsan-tsan da kuma lura da alamun zazzabin Lassa. Ba duk zazzaɓi ba ne zazzabin cizon sauro,” in ji ta.

Hukumar ta kuma bayar da rahoton aikin bayar da agajin gaggawa game da cutar a fadin ƙasar, inda ta ce aikin ya zama dole idan aka yi la’akari da ƙaruwar adadin wadanda aka tabbatar a fadin ƙasar.

Tun bayan ɓullar cutar ta karshe a shekarar 2016, hukumar lafiya ta yi nuni da cewa an samu karuwar masu kamuwa da cutar a ƙasar.

A halin da ake ciki a shekarar 2019, hukumar ta bayyana cewa an samu ɓullar cutar guda 796, yayin da a shekarar 2020, an tabbatar da adadin mutane 1,165 a ƙololuwar annobar.

NAN ta bayar da rahoton cewa ana tsammanin lamarin ya fi girma a lokacin rani (Janairu zuwa Maris), amma bayanan da aka tattara a Saliyo sun nuna ƙololuwar lokacin damina (Mayu zuwa Nuwamba).

Ana fitar da ƙwayar cutar a cikin maniyyi har tsawon watanni uku bayan kamuwa da cuta kuma masana ba su san yawan yaduwa ta hanyar jima’i ba.

Ana ƙoƙarin samar da rigakafin ta hanyar amfani da ƙwayar cutar zazzabin shawara.

Cutar zazzaɓin Lassa: NCDC ta sanar da mutuwar mutane 32 cikin makonni uku

A kalla mutane 32 ne suka mutu sakamakon cutar zazzabin Lassa a cikin makonni uku na farkon shekarar 2022, kamar yadda wani sabon rahoto da hukumar yaki da cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar.

Rahoton, wanda aka fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar daga 48 a mako na biyu na 2022 zuwa 74 a mako na uku, wanda ya wuce 17 zuwa 23 ga Janairu.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe