24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Matashi ya kone banki kurmus kan yaje neman bashi an hana shi

LabaraiMatashi ya kone banki kurmus kan yaje neman bashi an hana shi

Rundunar ‘yan sanda a kasar Indiya ta samu nasarar kama wani matashi da aka bayyana cewa ma’aikacin agaji ne da ya bankawa wani banki wuta a jihar Karnataka…

Wani mutumi mai suna Wasim Hazaratsab Mulla, dan shekaru 33, wanda rahotanni suka bayyana cewa ma’aikacin ba da agaji ne a birnin Haveri, ya dauki kafa ya tafi wani banki mai suna Bankin Canara dake jihar don neman a ba shi bashin Rupee miliyan 1.6 (kimanin Naira miliyan 9 a kudin Najeriya).

An hana matashin rance a banki

A rahoton da jaridar Aminiya ta ruwaito, mutumin yaje bankin a cikin watan Disambar shekarar da ta gabata, sai dai kuma cikin rashin sa’a bai samu wannan bashi ba, saboda matsala da ya samu a cikin takardun da ya bada, wadanda suka sabawa ka’idojin bankin.

A ranar Lahadi 9 ga watan Janairun shekarar 2022, an ruwaito cewa Wasim ya hau babur dinsa ya tunkari bankin, yaje ya bude wata taga ya fesa wani irin sinadari a ciki, sannan ya sanya wuta.

matashi ya kone banki
Ginin bankin ke nan lokacin da yake ci da wuta – Hoto Aminiya

An hango hayaki na tashi a cikin bankin

Wasu da lamarin ya faru akan idon su, sun bayyana cewa sun gano hayaki na tashi daga cikin bankin ne, sannan kuma kararrawa dake nuni da alamun akwai matsala na kara, sai suka yi gaggawar sanarwa da ‘yan sanda tare da kama Wasim suka tsare shi har sai da jami’an ‘yan sandan suka isa wajen.

A zantawar da manema labarai na kasar suka yi da wani jami’in dan sanda, ya bayyana musu cewa:

“Wasim ya fusata ne sakamakon hana shi cin bashi da bankin yayi. Ya bude tagar bankin ya fesa wani sinadari da yake ci da wuta, zai iya yiwuwa man fetur ne ya fesa, amma dai har ya zuwa yanzu muna nan muna cigaba da gabatar da bincike akan wannan al’amari.

“Shine shugaban wata kungiya mai zaman kanta, yaje bankin neman rancen kudin ne har Rupee miliyan 1.6, domin ya sayi wasu injuna. Sai dai abin farin cikin shine babu wani abu mai daraja da ya kone sanadiyyar wannan wuta da ya sanya,” in ji shi.

An yi asarar dukiya ta sama da naira miliyan 6 sakamakon wutar da ya sanya

Jami’an hukumar kashe gobara sun samu nasarar kashe wutar, sai dai kuma ‘yan sandan sun bayyana cewa, an samu asara ta kudi kimanin Rupee miliyan 1.2 (kimanin Naira miliyan 6 da dubu 641 da 920), inda kwamfutoci guda biyar, fankoki, fitilu, da na’urori, suka kone kurmus.

A yanzu haka dai ana tuhumar Wasim Hazaratsab Mulla da laifin kona wannan banki, kuma a yanzu haka yana jiran kotu ta yanke masa hukunci.

Abokai 3 da aka haifa shekara daya, suka yi makaranta daya, suke zaune a gida daya, sun mutu an binne su a waje daya

Abokan su uku, ‘yan shekara 22 sun kasance kansu daya, inda suke gudanar da rayuwarsu a Al-Khobar, sun rasa rayukansu ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da su. Sun kasance ‘yan asalin garin Damam ne.

  • Shafeeq:  Ya fito daga gundumar Malappuram ya kammala karatunsa wanda kafin mutuwarsa yana aiki ne tare da mahaifinsa mai suna Saidalavi Haji a wata cibiyar kasuwanci.
  • Ansif: Ya fito daga gundumar Wayanad, yana gaf da kammala karatunsa a Bahrain.
  • Sanad: Kuwa ya fito daga gundumar Kozhikode yana fafutukar komawa makaranta domin samun ilmi mai zurfi inda yake jiran a ɗage takunkumin tafiye-tafiye da aka kakaba saboda barkewar cutar Covid-19.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe