Dalibi daya na makarantar Bethel wanda ya rage a hannun ‘yan bindiga ya murje idanun sa, ya ce yana jin dadin zama da ‘yan bindiga saboda kayan tagomashin da yake samu a wurin su, Vanguard ta ruwaito.
Yayin da ‘yan kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, suka tattara kudin fansar da ‘yan ta’addan suka bukata, ‘yan bindigan sun damke wanda ya je kai sakon.
Shugaban CAN, reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph Joh Hayab kuma shugaban CAN na arewa da kuma Abuja ya bayyana damuwarsa akan dalibi daya da ya rage a hannun ‘yan ta’addan kasancewar sa mafi kankanta a cikin daliban da aka sace na makarantar Bathel a ranar 5 ga watan Yulin 2021 a makarantar wacce take kan babban titin Kaduna zuwa Kachia a karamar hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna, amma an saki dalibai 120.

Kamar yadda ya ce:
“Dalibin da ya rage a hannun ‘yan bindiga na makarantar Bethel Baptist ya na hannun ‘yan ta’addan. Dole mu bayyana gaskiya saboda kaxa a zarge mu, kasancewarsa karamin cikin su.
“Ina ganin ‘yan bindigan suna da wayau, sun yi masa dabarar da ya ji dadin zama tare da su. Har nama da kayan dadi suka dinga ba shi. Duk lokacin da suka fita sau sun siyo mishi tsaraba hakan ya sa ya ji dadin kasancewa tare da su.
“Idan suka ce ya wuce gida sai ya ki yarda saboda ya ce iyayensa suna dukan shi. Ba ma so mu fallasa iyayen sa, amma gaskiyar abinda ya ce kenan. Mu kan mu abin ya daure mana kai.”
A cewar Hayab wannan lamarin yana bukatar addu’ar daga jama’a. Don har wanda yake kai musu sako sun kama shi yayin da yake kokarin kai kudin fansar yaron.
Yanzu haka komai ya cakude gaba daya kuma dole ne kowa ya bi a hankali, a cewar shugaban CAN din.
Hayab ya dade yana bukatar hukumomi da su taimakawurin samun sun ga an sako yaran da aka yi garkuwa da su a Kaduna.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da malami da wasu mutum hudu – ‘Yan sanda
‘Yan sandan sun bayyana sunayen mutane biyar da aka yi garkuwa da su a jihar Yobe da ke arewa maso gabas a kasar Najeriya
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe a ranar Larabar da ta gabata ta tabbatar da sace Babagana Kachalla, mataimakin shugaban makarantar Central Primary Buni Yadi da wasu mutane hudu da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Madiya da ke karamar hukumar Gujba a jihar.
Kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.
Mista Abdulkarim, mataimakin sifetan ‘yan sanda ya bayyana sunayen sauran wadanda aka sacen da suka hada da Abubakar Barma, Haruna Barma, Modu Bukar da kuma Hajiya Gana.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: infor@labarunhausa.com