24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Mutane na ta cece-kuce bayan an jiyo Rochas Okorocha na jawo ayar Al-Qur’ani mai girma a wajen kamfen din shi

LabaraiMutane na ta cece-kuce bayan an jiyo Rochas Okorocha na jawo ayar Al-Qur'ani mai girma a wajen kamfen din shi

Idan ba a manta ba, Okorocha ya bayyana ra’ayin sa na takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC a wata takarda wacce ya tura wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Yayin jawabin sa, an ga sanatan yana janyo aya daga cikin Al’Qur’ani mai girma inda yace shi dan takara ne mai adalci kamar yadda Allah ya umarci yin adalci cikin Suratul Nahli.

Ya bukaci duk masu sauraron sa da su zabe shi don zai samar da sabuwar Najeriya. Okorocha wanda yanzu haka sanata ne mai wakiltar Imo ta yamma ya sha cece-kuce bayan janyo ayoyin Qur’ani.

Ga bidiyon a kasa:

Ga tsokacin ‘yan Najeriya bayan bidiyon nasa ya bayyana a Twitter:

babaidris090 ya ce:

“Sai Alhaji Rochas Okorocha, ya zama Sheikh Alrochas bin Okorocha yayin shiga jerin masu takarar shugaban kasa a 2023.”

Aucho00 ya ce:

“Au dama har Rochas so yake yi ya shugabanci Najeriya??”

Franklin_M_F ya ce:

“Ka ba ni damar zama maka matukan jirgin da zaka dinga zirga-ziga a sabuwar Najeriya. Kalli yadda Rochas Okorocha yake jan gemun sa da yatsu kamar shainadin da yake son tara aljanu don su yi masa aiki.”

DareGlintstone tace:

“Rochas ya ko sarki Martin Luther da karfi da yaji. Ba ni zaka yaudara ba.”

iam_leochizzy ya ce:

“Rochas ya ce shi Kyaftin ne wanda zai kai Najeriya sabon wuri. Haka Buhari ya yi mana alkawarin zai canja kasa. Yanzu ga Rochas ya yi. Ko ina zai kai mu oho? Kafin ya kai mu duhu.”

An cire Rochas Okorocha daga sarautar gargajiya a Kudu kwana 1 bayan ya ce zai gina Jami’ar Musulunci a Arewa

Sarkin Iselu, Oba Akintunde Akinyemi, ya janye kokarin nada sarautar gargajiya da yayi ga tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.

Haka kuma Sarkin ya dakatar da bikin nadin sarautar da aka sanya za ayi a ranar 19 ga watan Satumba.

Hakan dai ya fito a wata takarda wacce aka rubuta a ranar 9 ga watan Agusta, wacce Sarkin ya sanya hannu da sunan Okorocha a jiki.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe