29.5 C
Abuja
Friday, February 3, 2023

Bidiyon yadda aka gudanar da shagalin sunan jikar Jaruma Hafsat Idris (Barauniya) ranar Laraba

LabaraiKannywoodBidiyon yadda aka gudanar da shagalin sunan jikar Jaruma Hafsat Idris (Barauniya) ranar Laraba

Jarumar fina-finan Kannywood, Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya ta yi gagarumar liyafa a ranar Laraba bayan diyar ta wacce ta aurar a shekarar da ta gabata ta haihu.

Shagalin sunan wanda ya samu halartar manyan jarumai tsofaffi da sabbi yadauki hankali kwarai. Cikin jaruman da suka yi wa Hafsat kara akwai Rukayya Dawayya, Samira Ahmad, Mansura Isah da sauran su.

hafsatttt
Bidiyon yadda aka gudanar da shagalin sunan jikar Jaruma Hafsat Idris (Barauniya) ranar Laraba

Kamar yadda jarumaHafsat Idris ta wallafa bidiyoyi wadanda ta dauki wankan ban mamaki a shafin ta na Instagram, an ga sauran jarumai suna tikar rawa.

ta wallafa yadda aka sanya wa jaririyar suna ‘Hafsat’ wato takwarar ta wanda hakan ya yi matukar sanya ta farin ciki.

Ga wasu daga cikin bidiyoyin da ta wallafa:

https://www.instagram.com/reel/CZh26yQpTZ-/?utm_medium=copy_link
Yadda su Mansura Isah suka shiga taron cikin takun burgewa

Kamfanin UK Entertainment ya maka Hafsat Idris Barauniya a kotu

Babbar kotu mai lamba 18 da ke zama a garin Ungoggo ta na ci gaba da shari’ar fitacciyar jarumar fina-finai, Hafsat Idris Barauniya da kamfanin UK Entertainment.
Kamfanin na zargin jarumar da amsar musu kudin aiki N1,300,000 ba tare da karasa mu su aiki ba.
Mai shari’a, Zuwaira Yusuf ce ta ke gudanar da shari’ar. UK Entertainment sun bukaci ta biya su diyyar bata musu lokaci da ta yi.

Dama kamfanin ya bayyana yadda su ka mallaka wa jaruma Hafsat Idris kudaden sannan su ka bukaci ta yi musu wani aiki na TV Show, amma shiru suke ji tamkar malam ya ci shirwa.

Kamfanin ya zargi jaruma Hafsat Idris wacce aka fi sani da barauniya da kin yin aikin duk da amshe kudaden da ta yi ba tare da maida mu su ba.
Duk da dai jarumar ba ta halarci kotun ba, Hafsat Idris ta tura lauyanta don ya wakilce ta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com


Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe